Matawalle ya sha rantsuwa kan ba shi da hannu a matsalar tsaron Zamfara

Daga WAKILINMU

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi rantsuwa da Ƙur’ani kan cewa ba shi da wata alaka da ‘yan bindigar da ke addabar jiharsa.

Gwamnan ya ƙalubalanci mazauna jihar, da su ma su kwatanta shan ranstuwa kamar yadda ya yi domin tabbatar da cewa ba su da hannu cikin matsalar tsaro da ta addabi jihar.

Gwamnan ya yi hakan ne a ranar Lahadi a garin Gusau, babban birnin jihar yayin karɓar lambar yabo da Cibiyar Karatun Ƙur’ani ta Nijeriya ta ba shi a matsayin Khadimul Ƙur’an.

Ya ce kamar yadda ya sha faɗa lamarin rashin tsaron nan ba gwamnatin tarayya, gwamnoni ko jami’an tsaro kadai abin ya shafa ba, abu ne da ya shafi kowa kuma kada a saka siyasa cikinsa.

Gwamnan ya sha rantsuwa a kan ba shi da masaniyar matsalar kamar yadda ba shi da hannu a cikinta, haka ma bai san ko wane ne ki shirya hakan ba.