Matsalar ƙarancin abinci da ke kunno kai

A bayyane ya ke cewa illar da ambaliyar ruwa ta 2022 da ta addabi sassa daban-daban na Nijeriya ta fifa ƙasar cikin wani irin hali.

Don haka, ba abin mamaki ba ne cewa Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya faɗakar da ’yan Nijeriya da su tashi tsaye don havaka farashin abinci da haɗari a 2023 saboda wannan ambaliya da tsadar taki.

Cibiyar hada-hadar kuɗi ta duniya ta ce ƙara samun sauyin yanayi a cikin daidaiton farashin kasuwa da kuma cigaba da dogaro da kuɗaɗe da babban bankin ƙasar ke bai wa giɓin kasafin kuɗi na iya ƙara taɓarɓarewar farashin.

Duk da haka, Gwamnatin Tarayya (FG) ta yi watsi da sanarwar IMF. Ya ce bai kamata ’yan Nijeriya su ji tsoron duk wata matsalar abinci ba.

Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara ta Tarayya (FMARD) ta bayyana cewa ta tanadi matakan daƙile rikicin. Wani ɓangare na matakan, a cewar FMARD, ya haɗa da rarraba kayan abinci iri-iri daga tsarin tanadin abinci na FG ga marasa galihu da waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa ta hanyar Ma’aikatar Agaji ta Tarayya, Gudanar da Bala’i da Ci gaban Al’umma. Har ila yau, ana rarraba kayan amfanin gona da aka ba da tallafi kamar takin zamani, ƙwararrun iri da sinadarai na noma ga manoman alkama, shinkafa, da masara da abin ya shafa don noman rani.

Ma’aikatar ta ce ta kuma rarraba kayayyun kaji don maido da qananan kaji da abin ya shafa a faɗin ƙasar.

Akwai buqatar gaggawa ta komawa aikin noma, wanda ke da fa’ida a yanzu fiye da man fetur. Ya kamata gwamnati ta tafiyar da wannan tsari ta hanyar samar da yanayin da za a iya bunƙasa noma.

Misali, yakamata ta ba da tallafin kayan taki da tabbatar da cewa ta kai ga masu amfani da ƙarshen.

Ya kamata kuma ta ba da gyare-gyare da ƙarfafawa ga manoma na gida.

A nasu ɓangaren, manoma na buƙatar su rungumi sabon tsarin noma da fasahar ƙere-ƙere ke tafiyar da su tare da kawar da ɗanyen kayan amfanin gona. Suna kuma buƙatar rungumar amfanin gona mai yawan gaske, noma na kowane lokaci, da ingantattun wuraren ajiya.

Wassalam.

Daga MUHAMMAD AWWAL, 08062327373.