Matsalar jinyar ƙwaƙwalwa ce ke kai mata ga kashe mazajensu – Saratu G Abdul

“Matsalar ƙwaƙwalwa cuta ce da ba a fiya damuwa wajen magance ta ba”

“Ana yi wa matsalar ƙwaƙwalwa gurguwar ma’ana”

Daga ABUBAKAR M. TAHEER

Hajiya Saratu Garba Abdullahi ƙwararriya malamar jinya ce wadda ta ke koyarwa a Tsangayar Koyon Aikin Jinya na Jami’ar Bayero dake Kano. Sai dai a halin yanzu ta ke Ƙasar Amurka tana digirin na uku, wato PHD, kan Nursing Research. A cikin wannan tattaunawa ta musamman da ta yi da wakilin Manhaja a Haɗeja, ta kawo irin matsalolin dake damun ƙwaƙwalen mutane, waɗanda ke sanadin faɗawa a babbar matsala ko aikata aikin danasani ba tare da an ankara ba. Ta kuma ƙara bayyanai na hanyoyin da za a iya bi wurin ganin an magance matsalar, tun daga kan taimakon da gwamnati za ta iya bayarwa zuwa kan masu abin taimako. Idan kun shirya, a sha karatu lafiya:

MANHAJA: Za mu so ki gabatar mana da kanki ga masu karatunmu.

SARATU: Assalamu alaikum warahamatullah. Sunana Saratu Garba Abdullahi, wanda aka haife a Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu da ke Jihar Jigawa. Na yi digirina na farko a kan Aiki Jinya, wato ‘Bsc. Nursing’, sai kuma Msc. akan ‘Community health Nursing’. Na kuma yi MBA akan ‘International Hospital Administration’. Baya ga haka, na samu ‘Certificate’ akan ‘Cognitive Behavioral Therapist’ Inda nake aiki wajen duba masu fama da matsananciyar damuwa, ‘post Traumatic Stress Disorder PTSD, Depression da Anxiety’.

Haka kuma Ina ci gaba da karatun digirina na uku a jami’ar Saint Louis University Valentine School of Nursing Saint Louis, Missouri USA.

Za mu so ki mana bayani kan matsalar ƙwaƙwalwa da ake fama da ita?

To, jinyar ƙwaƙwalwa wata matsalace da ta ke shafar ƙwaƙwalwan mutum wanda kuma hakan yakan shafi yin tunani mai kyau daga mutum. Ita wannan jinyar dama tun can akwaita ba yanzu aka fara ta ba, sai dai mutane ne ba su waye da ita ba.

Kasancewar ta jinya wata kala wanda ba a fiye son yin magana a kanta ba, saboda wasu suna kallon matsalar da gurguwar ma’ana, a ganin su, Idan akace matsalar ƙwaƙwalwa to, hankali ya tattara ne akan ana nufin mahaukaci, wanda ke yin sananniyar hauka. Wanda yake yawo da kaya a yage ko yake wani abu wanda da zarar an ganshi anga mahaukaci, sai dai maganata ta gaskiya ba haka ba ne.

Matsalar ƙwaƙwalwa takan iya samun mutum ta hanyoyi da dama, kamar matalar gado, wato ‘Heridity’ a Turance, wanda Idan akwai matsalar a cikin dangin mutum za ka ga shima ya gaje ta, kamar kaka ko baban mutum wanda ke fama da matsalar za ka samu wani a dangi ya samu nasa kason na ita jinyar.

Ta daya janibin kuma ana iya samun jinyar ƙwaƙwalwa ta faruwar wasu abubuwa marasa daɗi ga mutum, kamar mutuwar makusanci wanda ya zama an shaƙu da shi, ko asarar dukiyoyi kamar gobara ko gona ko matsalar yara marasa jin magana, koma matsala ta auratayya tsakanin miji da matarsa da dai sauran su.

Haka kuma ko a gun aiki idan mutum ya kasa shawo kan wata matsala wannan sai ya saka masa cutar da ake kira ‘Depression’, wato cutar damuwa ko kuma mu ce ƙunci, inda mutum zai ji kamar ya kashe kansa don baƙin ciki. Haka kuma akwai ciwo irinsu ‘skizopedia’, akwai ‘Maneaa’ da dai sauran su. Duk waɗannan ciwuka ne dake damun ƙwaƙwalwan mutane. Kuma za ka iya gane kana ɗauke da ɗaya daga cikin su ne ta hanyar ziyartar likita don ya duba ka, kuma shi ne zai ɗora ka akan magunguna da shawarwari da za a iya samun sauƙi.

Idan ka yi duba da ƙasa irin tamu, mutane ba su cika mayar da hankali wurin samun wayewar kai kan irin wannan matsala ba, wanda hakan ke sa ba za su ma san suna ɗauke da cutar ba, bare ayi zancen zuwa aga likita don neman magani ba.

Idan ka yi wa matsalar kashe miji da mata ke yi, ko mutum ya kashe kansa kallon ilimi, za ka tarar da matsalar jinyar ƙwaƙwalwa ce ke zama sanadi.

Yawanci za ka tarar matsalar damuwa ce, wato depression idan mutum ya samu kansa a ciki, yayin da ya shiga mawuyacin hali, kuma wannan matsala na tare da shi, zai ji wani abu a ƙwaƙwalwarsa na gaya masa “ai ni ba ni da wani amfani, rayuwata ba ta da muhimmanci, menene amfanin zamana a duniya.”

Ko kuma “mijina ne shamaki tsakani na da samun kwanciyar hankali, shi ne kawai mai dasa min damuwa, idan ya mutu walwalata da farin cikina zai dawo.” Da dai makamantar su. To idan tunanin ya ci gaba da yawo a ƙwaƙwalwa, kuma abinda ake yi mata da ke haifar da cutar ta damuwa na ci gaba, ma’ana dai cutar na ƙaruwa ko dai ta sanadiyyar yawaitar matsalolin ko rashin kwaɓa daga ɓangaren rashin zuwa asibiti, zai ba wa wannan tunanin damar yin tasiri, har a waye gari mai wannan matsala ya amince da cewa, ba shi da wata mafita sai ta ɗaukar ransa da kansa, ga mace, kashe mijin nata don matsalar ta sa mata amincewa ba wata mafita sai ita, matuƙar tana buƙatar hutu.

Duk da cewa, baya ga matsalar damuwa, akwai matsalar ƙwaƙwalwa mai zaman kanta da ka iya sa mutum ya illata kansa ko makusancin sa ba tare da wani ƙwaƙwaran dalili ba. Ita wannan matsala ana kiranta da OSD a likitance. Jinya ce da ke dasa burin ganin mai ita ya illata duk wani makusancin sa. Misali, matsalar da za ka ji wani ya illata yayansa na jini, kuma idan ka bincika sai ka tarar da tarin soyayya a tsakanin su. Ko kuma mata ta nemi illata mijinta dake matuƙar ƙaunar ta, ko ta yi yunƙurin hallaka ‘ya’yan da ta haifa da cikinta duk da soyayyar da ke tsakanin uwa da ‘ya’yanta. Ko ɗa ya illata iyayensa ba tare da suna muzguna masa ba.

Idan kuwa mutum na fama da irin wannan matsala bai kamata a zura masa ido ba, ko a nemi rufe shi a xaki ko makamantan su, kamata ya yi a kai shi ga likitocin ƙwaƙwalwa, bayan bince da za su yi masa, za su ɗora shi kan maganin da ya dace da matsalar sa.

Ta waɗanne hanyoyi ne mutum zai iya gane yana fama da ɗaya daga cikin matsalolin ƙwaƙwalwa?

To, ta inda mutum zai gane yana da wannan matsalar akwai alamomi kamar mutum yana kallon kansa a matsayin ba komai ba, duk abinda ya cimma yana kallon sa a matsayin bai kai wani matsayin ba. Ko kuma yana kallon kansa a matsayin marar amfani a cikin al’umma, yana yawan jin ƙunci a ransa.

Da zaran ka ji xaya daga cikin waɗannan ko masu kama da su, to maza ka garzaya asibiti, kaga likitin da ake kira da “Phcytiric doctor” a Turance.shi ne zai ma ka gwaje-gwajen da suka kamata tare da tambayoyi masu dama, kafin ya gano idan akwai matsalar tattare da kai, sannan ya ɗora ka kan magani da shawarwarin hanyoyin da za ka bi don tafiya tare da maganin.

Shin ana iya warkewa daga cutar ta ƙwaƙwalwa?

Ƙwarai da gaske, za a iya warkewa garau daga mafiya yawa daga cutukan ƙwaƙwalwa, idan an bi hanyoyin da suka dace. Tun daga duba da yanayin ƙasashen da suka cigaba suke tarbar matsalar tun a matakin yarinta. Kaga anan Amurka, za ka ga hatta a makarantun ‘Elementary’, malamai na sa ido sosai akan yara ta vangaren fahimtar ɗabi’u da ke da alaƙa da halin da ƙwaƙwalwa ke ciki.

Duk yaron da suka fahimci ɗabi’arsa ta bauɗe, wato ta fita daga sananniyar ɗabi’a ta masu shekarunsa, za su yi iya ƙoƙari wurin ganin an kai su asibiti don tarbar matsalar da wuri, don ganin sun samu sauƙi.

A ɓangare ɗaya, akwai taimako ta fuskar tattaunawa da masani kan matsalar, abinda ake kira da ‘Counseling’, ko ƙarfafawa. Hanya ce ta gyara gurɓataccen tunani da ƙwaƙwalwa ke wa mai matsalar aike da su, ta hanyar ba shi damar ya amaye ƙuncinsa, ya faɗi nufinsa da abin da yake yunƙuri, shi kuma masani kan wannan ɓangare zai yi amfani da hanyoyi da ilimin matsalar ya sanar da shi don saisaita tunanin mai matsalar da karkatar da shi kan inda ya kamata ya nufa wanda zai kai shi ga hanyar waraka.

Wannan ɓangare kan taimaka matuƙa, duk da cewa, a ƙasa irin tamu ba a cika ɗaukar shi da muhimmanci ba, sai dai Ina mai bada shawarar mu gwada, domin hanya ce da zata iya kawo mana sauƙin ababe da dama. Sannan yana da matuƙar muhimmanci mu san cewa, likita ne kawai zai iya ba ka maganin da ya cancanci matsalarka.

Kada ka ce don wani ya je asibi, likita ya ba shi magani, kai kuma kana jin irin abin da shi yake ji, ma’ana alamomin da ku ke ji sun yi kamanceceniya, don haka sai ka ɗauki sunan irin maganin da yake sha, ka siya. Wannan ba hanyar waraka ce ka ɗauka ba, domin duk da kama da matsalolinku ke yi, zai iya yiwa abin da ke damunku ya bambanta. Don likita za ka je kaima ka gani, ya yi ma ka naka binciken, sannan ya baka irin maganin da ya dace da matsalarka. Matuƙar kana son samun sauƙi wannan ce hanyar.

Kafin nan kuma shi likitan zai duba yaga shin ma menene ya jawo ma ka wannan jinyar, don yin yadda ya kamata don tabbar da an kau da matsalar, wanda hakan zai sa maganin ya yi aikin yadda ake fatan samu daga gare shi.

Ta hanyar bin waɗannan matakai yadda ya kamata, za a iya samun waraka ta gabaɗaya, kaga mutum tamkar bai taɓa yin jinya irin ta ba.

Hajiya Saratu

A ɓangaren ‘yan’uwa ko makusanta na mai fama da cuta irin ta ƙwaƙwalwa, ko akwai taimakon da za su iya bayarwa ta fuskar samun lafiyar mai lalurar, ko kuwa wannan fage kawai na likitoci ne?

A ɓangaren makusantan mai wannan matsala ta ƙwaƙwalwa, suna da muhimmiyar rawa da za su iya takawa ta fuskar masun lafiyar makusancinsu da ke fama da lalurar ta ƙwaƙwalwa. Abu na farko, akwai buƙatar a janyo su a jiki, fiye da na sauran mutane, a yawaita kwantar masu da hankali tare da yi masu uzuri kan wasu ababe da suke aikatawa. A dai ba su kulawa ta musamman da ta bambanta da ta saura kamar yadda matsalarsu ta fitar da su daban da sauran mutane.

Mu a ɓangaren mu, idan aka kawo mutum asibiti, to muna ƙoƙarin ba wa ‘yan’uwansa dama su matso kusa da shi sosai, don ya samu sakewa tare da kwanciyar hankali, hakan zai taimaka wurin ba mu irin haɗin kai da muke buƙata daga wurin shi marar lafiyar.

Baya ga haka, yana da matuqar muhimmanci ‘yan’uwan mai tare da wannan jarrabawa su yawaita nanata masa muhimmancin sa gare su da al’umma gabakiɗaya. Yadda rayuwarsa ke iya kawo cigaba a tsakanin mutane da kuma ƙuncin da za su iya shiga idan suka rasa shi. Wannan zai taimaka masa tare da ba shi ƙwarin gwiwar yaƙi da cutar don ganin ya samu sauƙi.

Kuma ta ɓangaren lokutan da zai dinga ganin likita, ya kasance makusantan nasa ne suka ɗauki nauyin kula da lokacin, nasa kawai taso mu je, haka kuma ta ɓangaren shan magani, ya kamata su kula ko ya sha.

Ko akwai wani taimako da ya kamata likitocin su yi wa makusantan masu lalurar ƙwaƙwalwa ta fuskar wayar da kai?

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.