Matsalar kuɗi: Wani kamfanin Afirka ta kudu ya shirya adabo da Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

Wani kamfani asalin Afirka ta Kudu wanda yake gudanar da kasuwancinsa a Nijeriya ya shirya tsaf don barin Nijeriya.

Jaridar Ripples Nigeria ta rawaito cewa, shi dai wannan kamfani sunansa Southern Sun. Kuma shi ne kamfanin da ya mallaki rukunin otal-otal ɗin Southern Sun Hotel.

Shi dai wannan kamfani tuni ya yi gwanjon rukunin otal-otal ɗinsa na Southern Sun Hotels dake yankin Ikoyi dake jihar Legas domin ya biya bashin da ake bin sa.

Wata majiya ta bayyana cewa, tasirin annobar COVID-19 ta kawo naƙasu ga kuɗin shigar da kamfanin yake samu. A ƙoƙarinsa na rage asarar, kamfanin ya yanke shawarar sayar da kaso 75.55 na hannun jarinsa a kamfanin ga kamfanin Kasada Albatross Holding a kan farashin Dalar Amurka miliyan $30.4.

Ana sa ran kamfanin zai amfani da waɗancan kuɗaɗen na sayar da kamfaninsa a Nijeriya don bunƙasa kamfanin nasa da yake a ƙasar Mozambique.

A halin yanzu dai shirye-shirye sun yi nisa na cinikin a yanzu abinda ake jira kawai shi ne, Sahalewar hukumar kare haƙƙin mai saye, (FCCPC) da na hukumar canji (SEC).

Haka nan wata majiya mai tushe ta bayyana cewa, sabon mallakin otal ɗin zai canja masa suna daga Southern Sun Hotels zuwa Novotel.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *