Matsalar rashin aiki ta fi ƙamari a mulkin Buhari – Bankin Duniya

Daga UMAR M. GOMBE

Wani sabon rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa, a tarihin Nijeriya matsalar rashin aiki ta fi ƙamari ne a gwamnatin Buhari.

Rahoton ya ce matsalar rashin aikin ta fi shafar matasan Nijeriya ne da kashi 42.5 cikin 100, yayin da ‘yan gaba da matasan ke da kashi 26.3 cikin 100.

A cewar rahoton, a halin da ake ciki matsslar rashin aikin yi a Nijeriya ta tumbatsa har ninki biyar daga kashi 6.4 a 2010 zuwa kashi 33.3 a gaɓar ƙarshe ta 2020 kamar yadda rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ya nuna.

Rahoton ya ce matsalar rashin aikin a Nijeriya wadda ta soma girma a 2015 lokacin da Buhari ya kama mulki, ta ƙara tsananta ne sakamakon annobar korona da ta addabi ƙasar.

“Ƙaruwar rashin aikin yi ya yi ƙamari ne tun koma bayan tattalin arziki da aka samu a 2015 zuwa 2016, sannan lamarin ya tsananta sakamakon ɓullar annobar korona 2020,” in ji rahoton.

Rahoton wanda aka wallafa tare da haɗin gwiwar asusun RSR da KWPF, ya nuna cewa maza marasa aikin yi a Nijeriya sun kai kashi 46.4 cikin 100, yayin da mata kuwa ke da kashi 40.6 cikin 100.

Bankin Duniyar na ra’ayin cewa, yawan ƙetarawa neman arziki a ƙetare da ‘yan Nijeriya kan yi, hakan na da alaƙa da matsalolin da suka dabaibaye tattalin arzikin ƙasar.

Bankin ya ce daga 1990 zuwa 2019, adadin ‘yan Nijeriya masu fita waje ya ƙaru daga 446, 806 zuwa 1,438, 331.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *