Matsalar rashin tsaro; ɗan leƙen asiri ya fi ɗan ta’addar daji iya ta’adanci…

Daga MUHAMMAD AMINU KABIR

Lamarin rashin tsaro yana ƙara ƙamari ne ta sanadiyyar wasu daga cikin Al’umma da har yanzu suke ɗaukar bayanan sirri ko dai na jama’ar gari, ko kuma na Jami’an tsaro suna kai wa varayin daji. Wannan yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa lamarin nan ya ƙi ci, ya qi cinyewa.

A kullum Jami’an tsaro suna bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an magance wannan matsalar ta rashin tsaro, amma kuma wasu ɗaiɗaikun mutane da rashin tsoron Allah ya hana su barin wannan mummunar ɗabi’ar ta ɗaukar bayanai su kai wa ‘yan ta’adda. Abin takaici baka iya cewa ga waɗanda suke yi sai dai idan Allah ya tona masu asiri.

A wasu wuraren ma, za ka tarar cewa, ko dai saboda barazana da ɓarayin suka yi wa mutanen yankin ko kuma dai wata yarjejeniya ce tsakaninsu, za ka tarar sun ma fi yadda su haɗa wa ɓarayin kuɗi domin su basu kariya ko kuma su ƙyale su domin su ci gaba da ayyukan su na yau da kullum.

Ko a ɗan tsakanin nan an kama mutane huɗu da ake zargin sun taimaka wajen kai harin gidan gyaran hali dake Kuje Babban birnin Tarayya Abuja, rahotannin da suke ta yawo sun nuna cewa Jami’an tsaron Najeriya sun cafke wasu mutane huɗu da ake zargi da kwarmata bayanan sirri ga ‘yan bindiga, an kuma kama su da wayoyin salula da basu amfani da yanar gizo-gizo da ma wasu na’urori.

Ko a jihar Katsina ma haka lamarin yake, kusan duk lokacin da mai magana da yawun Rundunar ‘yansandan Jihar SP Gambo Isah ya gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban manema labarai za ka tarar cewa an kawo wasu mutane da suke kai wa ‘yan ta’addar kwarmato. Irin waɗannan mutanen za ka tarar da su talakawa ne ana tare da su, amma kuma suna ha’intar jama’a tare da kwashe bayanai suna kai wa ɓarayin daji.

Babban abinda yake ɗaure kai a nan shi ne, irin waɗannan mutanen ba ka samun Labarin wane takamaimai hukunci a ka yi masu, wanda zai aike da saƙo a cikin al’umma da har za su gane cewa aikata irin wannan lamarin ɓarna ce babba, domin su kauce ma aikatawa. Sau tari irin wannan rashin bayyana hukuncin shi ne yake sanyawa wasu ma su faɗa aikata varna.

Kodayake, a vangare guda kuma, wasu daga cikin mutanen da ake kamawa ɗin suna bayyana cewa, tsananin talauci ne yake sanya su tsunduma irin wannan aikin. Ganin cewa Lamarin tattalin arziki ya taɓarɓare a faɗin ƙasar nan, ga kuma yanayin rashin tsaron da tashin hankali, ga Iyali da sauransu. Kodayake, wannan ba wani uzuri ba ne da zai sanya mutane su faɗa Aikata varna ba, amma dai zai yi tasiri wajen ingiza su aikatawa cikin sauƙi.

Shin wanne yunƙurin Gwamnati take yi wajen ganin ta shawo kan wannan matsalar ta rashin tsaro? Ganin cewa yanzu lamarin yana ta ƙara zama wani irin, banda ‘yan ta’adar da suke ta’adanci, ga kuma jama’ar gari su ma suna afkawa cikin wannan mummunar ɗabi’ar ta ɗaukar bayanai su kai wa ‘yan ta’addar su kuma su zo su ɗauki mutane tare da neman kuɗin fansa.

Kusan duk mai lura da al’amurran yau da kullum zai fahimci cewa, zai yi wuya a ce baƙo ya zo daga wani wuri ya shigo har cikin jama’a ya yi ta’asa, kuma har ya fita ba tare da taimakon wasu daga cikin al’ummar wurin ba.

Lamarin nan fa na samar da tsaro aiki ne na kowa da kowa, matuƙar dai al’umma ba su daina ba da bayanan sirri ga waɗannan Mutanen ba, to babu ranar ƙarewar wannan lamarin, sai dai a yi ta tubka da warwara. Jami’an tsaro na ƙoƙarin tunkarar ‘yan ta’addar, jama’ar gari kuma na ba su bayanai a kan junansu da kuma Jami’an tsaron.

A mafi yawancin lokuta, za ka ga an kai wa Jami’an tsaro hari ko a ce an yi musu kwanton vauna. Hakan baya rasa nasaba da bayanan tafiyar su da ake baiwa ‘yan ta’addar wanda hakan ba ƙaramin illa yake yi ba ga tsaron ƙasa da kuma rayukan Jami’an tsaronmu.

Lamarin rashin tsaron nan ya sa ana ta asarar rayukan jama’a a sassan ƙasar nan daban-daban. Na baya-bayan nan shi ne, harin da ‘yan Ta’adar suka kai wa wata motar sufuri a hanyar Jibia ta jihar Katsina Inda suka halaka direban suka raunata wasu fasinjoji tare kuma da ɗaukar kuɗaɗe da wayoyin salular jama’a.

Hakakazalika, ‘yan Ta’adar sun kai wani harin Ta’adanci a shingen binciken ababen hawa dake zuma rock a kan Titin zuwa Abuja, duk wannan yana zuwa ne bayan wani harin kwanton vauna da aka kai wa Jami’an tsaron a Bwari yayin da suke sintin bada tsaro a Makarantar Horon aikin Lauya dake Bwarin duk a Abuja babban birnin Tarayyar Nijeriya.

Daga ƙarshe, muna addu’ar Allah duk wanda yake da hannu a kan wannan lamarin na rashin tsaro ko wanene Allah ka yi mana maganinsa alfarmar Sayyadina Rasullullahi Sallallahu Alaihi wasallam Amin.

Muhammad Aminu Kabir ya rubuto ne daga Katsina.
Adireshin Imel: [email protected]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *