Matsalar tsaro a Arewa: Manoma a yankunan karkara suna ƙara fuskantar matsala a daminar bana

Daga NAFI’U SALISU

Al’amarin rashin tsaro a Arewacin Nijeriya, abu ne da ya daɗe yana ci wa al’umma tuwo a ƙwarya, wanda kuma ya haifar da rashin kwanciyar hankali, walwala da shiga halin ni ‘yasu musamman a yankunan karkara da ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka.

Ayyukan ‘yan bindiga da garkuwa da mutane, ya yi sanadin rasa rayukan miliyoyin al’umma, tare da dukiya mai tarin yawa, da kassara ayyukan noma da kiwo a karkara. Hakazalika, ayyukan ‘yan bindigar ya yi sanadin lalacewar dubban garuruwa da a yanzu haka suka zamo kufai babu kowa a cikinsu, yayin da waɗanda suka yi gudun hijira don tsira da rayuwarsu suka cika birane don neman abin mafaka tare da abinda za su ci.

Gwamnatin baya da ta shuɗe, ta sha yin vavatu da kausasan maganganu a kafafen yaɗa labarai da jaridu a kan cewa tana yin nasara da yaƙin da take yi da ‘yan ta da ƙayar baya, to sai dai za a iya cewa abin tamkar shirin wasan kwaikwayo, don har yanzu mutanen da suke yankunan da ‘yan bindiga suka yi ka-ka-gida suna fuskantar cin zarafi daga masu ɗauke da makamai suna aikata ta’addanci.

Jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, Kaduna, Neja da Kebbi, jihohi ne da ayy ukan ‘yan ta’adda ya mamaye, kuma har yanzu waɗannan jihohi suna fuskantar matsalolin rashin tsaro dangane da ayyukan ‘yan bindiga.

A cikin jihar Katsina, ayyukan waɗannan ‘yan bindiga ya faro ne daga ƙaramar hukumar Batsari, wadda ke kewaye da ƙananun garuruwa da dama, kuma a waɗannan garuruwa mutane sun fuskanci hare-haren ‘yan bindiga da ya yi sanadin rasa rayuka da dama, da asarar dukiyoyi, baya ga tasar wasu ƙauyuka da dama. Dubban mutane ne suka yi ƙaura daga garuruwan da suka fuskanci hare-haren ‘yan bindigar, suke kuma ci gaba da ƙara fuskantar wasu sabbin hare-haren a halin yanzu.

Jihar Zamfara da ke makwaftaka da jihar Katsina, wadda ita ce babban tushen waɗannan ‘yan bindiga. Har yanzu babu wasu alqaluma na adadin rayukan da aka rasa, baya ga dukiya da sauran abubuwa na amfanin yau da kullum. Sai jihar Sokoto, Kaduna, Neja da Kebbi da su ma ayyukan ‘yan bindigar da garkuwa da mutane da ya jefa miliyoyin mutane cikin tsaka mai wuya, baya ga waɗanda suka mutu.

A halin yanzu a waɗannan jihohi musamman jihar Kaduna, ayyukan ‘yan bindigar yana taka rawa sosai wajen yi wa manoman yankin barazana. Manoman karkara sun yi shuka, sun kuma saka amfanin gona sosai, musamman duba da yadda kayan masarufi yake tsada, to amma kuma barazanar ‘yan bindiga ta sa wasu manoman da dama tafka asarar shukar da suka yi, wanda wasu har yanzu ba su samu damar yin shuka a gonakinsu ba, wasu da suka yi tun farkon damina kuwa ‘yan bindigar sun tura dabbobinsu sun cinye.

Bayan haka, manoman wannan yanki suna matuƙar fuskantar cin zarafi daga ‘yan bindigar, inda suke shigowa cikin garuruwansu da dare suna fasa musu shagunan (Provisions) suna kwashe musu kaya, sannan da safe idan sun tafi gonakinsu don yin aiki sai su kora su zuwa nasu gonakin tare da tilasta su a kan su yi musu aiki.

Ko a satin da ya gabata, ‘yan bindigar sun ɗauki wani babban mutum (attajirin manomi) da suka daɗe suna ɗana masa tarko. Wata majiya ta bayyana cewa, shi kaɗai yana noma sama da buhun hatsi miliyan ɗaya idan kaka ta yi, domin yana da gonaki da dama. Hakazalika, ‘yan bindigar sun nemi kuɗin fansa a kan attajirin ƙauyen, an kuma kai musu amma sun ƙi sakin sa sun ce sai an ƙara kai musu Naira miliyan bakwai.

Duba da irin yadda mutanen karkara suka sadaukar da rayuwarsu suke noma abinda ƙasa za ta ci, amma har yanzu Gwamnatin Nijeriya da jami’an tsaro sun kasa samar wa da mutanen karkara mafita, haka ake shiga ana kama su ana musu kisan gilla tare da kwashe musu dukiyoyi wani lokacin ma har a ƙona musu amfanin gona tun yana gonar ba su cire ba, wani lokacin a tura dabbobi ciki su cinye, wani lokacin kuma a gidan za a ƙona musu rumbunan hatsi saboda ta’addanci.

Ire-iren waɗannan ayyukan ta’addanci ne suke haifar da mutum ya rataye kansa ya mutu, ko kuma ya sha wata guba ya mutu. Shin idan Gwamnatin Nijeriya ta rasa manoma a karkara, ko kuma aka ƙyale waɗannan ‘yan bindiga suka lalata karkara, suka hana noma da kiwo, shin ya ya ƙasarmu za ta zama? Tabbas rashin magance wannan matsala ta kawo ƙarshen ‘yan bindiga, babbar barazana ce ga tattalin arzikin ƙasarmu Nijeriya, kuma hakan zai ƙara jefa mu cikin yunwa da fatara.

Ana ganin yadda ‘yan gudun hijira suke ƙara kwararowa cikin birane suna neman matsugunni da ayyukan yi amma su kan rasa, ko da sun sami matsugunin da za su zauna amma aikin yi yana musu wahala. Hakan kuma yana ƙara jefa al’umma cikin talauci da taɓarɓarewar tattalin arziki, domin a cikin waɗanda suka nemi aikin yi suka rasa a kan samu waɗanda suke shiga miyagun hanyoyi irin su; fashi da makami, sata da shan miyagun ƙwayoyi da suke vatar musu da hankali su kama aikata ta’addanci.

Don haka ya kamata sabuwar Gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ɗaura ɗamarar yaƙar ta’addanci da masu aikata shi a Nijeriya, ta yadda ƙasarmu za ta samu ta farfaɗo daga zazzaɓin da ta shiga na karyewar tattalin arziki, da rashin abinci da ayyukan yi ga ‘yan ƙasa. Domin kwararowar mutanen karkara cikin birane ba alkairi ba ne, hakan yana da matuqar illa sosai. Mutanen karkara su ne suke yin noma, noman da ke samar da abinci mai yawa a cikin ƙasar nan, kuma a karkara ne ‘yan bindiga suke cin karensu babu babbaka.

Sannan mutanen karkara ba sa cin moriyar ayyukan raya ƙasa kamar mutanen cikin birni, domin wasu ƙauyukan hatta da asibitin sha-ka-tafi babu, babu wutar lantarki, ba ruwan sha, babu hanya mai kyau, babu makaratun boko, idan ma akwai to malaman ba sa bayar da ingantaccen ilimi ga mutanen karkara. Don haka wannan dalili ne ya sa za a iya kallon mutanen karkara a matsayin saniyar ware da ba sa samun kulawar Gwamnati.

Idan har wannan Gwamnati ta Bola Tinubu da gaske take, to ya kamata ‘yan Nijeriya mazauna karkara su samu zaman lafiya, ta yadda za su ci gaba da yin nomansu da kiwon dabbobi, kuma ya kamata Gwamnati ta tashi tsaye wajen inganta harkar noma domin abinci ya wadata a ƙasa. Idan ba haka ba, to lallai babu ko shakka Nijeriya za ta ƙara yin baya ta fuskar ƙarancin abinci, wanda kuma hakan babban ƙalubale ne ga Nijeriya.

Nafi’u Salisu (Marubuci/Manazarci) ya rubuto ne daga jihar Kano. nafi’[email protected] [email protected] 08038981211

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *