Matsalar Tsaro: Atiku ya yi kira da a dauki tsauraran matakai

Atiku ya koka akan harin da aka kaiwa sarkin Kiyawan Kaura

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya koka akan harin da wasu yan bindiga su ka kaiwa tawagar sarkin Kiyawan Kaura Alhaji Sunusi Muhammad Asha, a Giwa kan hanyar sa ta komawa Kauran Namoda daga Abuja.

Da yake taya sarkin jaje, akan wannan waki’a da ta fada masa, Atiku ya ce yawan kashe kashen da ake da zubda jini a kasar nan abin ya wuce hankali. Ya ce “ya zama wajibi a dau matakan hana wannan aika aika da yan bindiga su ke, abinda har ya kai a yanzu mutane na tsoron su fito daga gidajen su”

“Yin Allah wadai da abin ba zai isa ya hana aukuwar hakan a nan gaba ba, dole sai jami’an tsaro sun tashi tsaye sun dau matakai masu tsauri akan wadannan yan bindiga” inji wazirin Adamawan.

“Ya zama wajibi hukuma ta maida himma wurin hukunta masu laifin, domin ya zama izna ga na baya, in kuwa ba haka ba, to ba za a daina wannan ta’addanci ba”

Daga karshe ya taya iyalan wadanda suka rasu alhinin abinda ya faru, tare da sarkin Kiyawan Kaura da kuma al’umar jihar baki daya.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*