Matsalar Tsaro: Gwamna Bello ya haramta cin kasuwanni kara, sayen fetur a jarka a faɗin Neja

A matsayin wani mataki na yaƙi da matsalolin tsaro a jihar Neja, Gwamnan Jihar, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya kafa wasu sabbin dokoki da za su taimaka wajen kawo ƙarshen ƙalubalen tsaro da jihar ke fama da su.

Sabbin matakan tsaron da Gwamna Bello ya sanar a ranar Laraba, ya ce za su soma aiki ne daga ranar 1 ga Satumban 2021.

Waɗannan matakai sun hada da haramnta cin kasuwanni dabbobi na mako-mako a faɗin jihar, dole duk motar da za ta shigar da dabbobi cikin jihar ta nuna shaidar inda dabbobin suka fito da inda aka sayo su da kuma inda za a kai su.

Haka nan, daga yanzu an hana sayen fetur a jarka da makamantan haka a gidajen man da ke faɗin jihar, ba a yarda a saida wa abubuwan hawa da mai sama da na N10,000 ba a take, an hana zirga-zirgar manyan motoci masu jigilar itatuwa da katakai a jihar.

Kazalika, Bello ya ce daga yanzu babura a faɗin jihar za su riƙa aiki ne daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.

Ya ce, “Gwamnati na sane da irin halin da jama’ar jihar za su shiga sakamakon waɗannan sabbin matakan, sai dai an yi hakan ne don amfanin al’ummar jihar.”

Daga nan, ya ce gwamnati ta yi tir da yadda ɓarayin mutane da ‘yan fashin daji suka addabi sassan jihar, tare da jaddada ƙudurin gwamnatin na kakkaɓe ‘yan ta’adda da harkokinsu a faɗin jihar.

Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed I. Matane, ya fitar ta nuna gwamnatin jihar ta yi kira ga jama’ar Neja da su zama masu lura da kuma ankarewa game da sha’anin tsaro, sannan su kai rahoton duk wani al’amari da ba su gamsu da shi ba ga hukuma.

Gwamna Bello ya ya ƙara da cewa, lamarin tsaro abu ne da ya shafi kowa, don haka ya ce ya zama wajibi a haɗa hannu don tallafa wa ƙoƙarin gwamnati wajen yaƙi da matsalolin tsaron da suka addabi jihar don ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

A ƙarshe, Bello ya bai wa hukumomin tsaro umarni kan tabbatar da jama’ar jihar sun yi biyayya ga sabbin dokokin da aka shimfiɗa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *