Matsalar Tsaro: Makarfi ya gargadi ‘yan Nijeriya

Daga Aisha Asas

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Sanata Ahmed Mohammed Makarfi, ya ja hankulan ‘yan Nijeriya a kan su daina barin son zuciyarsu yana tasiri wajen daukar matakai wanda hakan ka iya haifar da rikici.

Makarfi ya nuna bukatar da ke akwai ‘yan Nijeriya su fahimci cewa matsalar tsaron da ke addabar kasar nan aba ce da ke bukatar a yi mata taron dangi domin dakile ta.

Yana mai cewa, “Wannan matsala ce da ta shafe mu baki daya.”

Makarfi ya yi wadannan bayanan ne a wata sanarwa da ya fitar inda ya nuna damuwarsa kan tabarbarewar sha’anin tsaron Nijeriya.

Ya ce, “Idan muka soma bin ra’ayoyinmu wajen daukar matakai wanda hakan kan haifar da wasunmu daga sassan kasa suna furta maganganun da ka iya harzukarwa, wannan wata alama ce da ke nuni da an kauce wa alkibla.

“Don haka ina kira a gare mu baki daya da cewa idan aka yi nazari za a a fahimci wannan matsalar ta shafi kowa wadda sai mun hada kawunanmu kafin mu iya kawar da ita.

“‘Yan siyasa da sauransu, wajibi ne mu kiyaye kada a siyasantar da batun tsaro, mu sani dole sai mun samu kasa kafin a yi batun siyasa.”

A cewarsa, “Daga jerin kalubalan da muke fuskanta, babu wanda ya fi ba ni tosro kamar matsalar lalacewar sha’anin tsaro a mafi yawan sassan kasar nan. Wanda batun samar da tsaro kuwa shi ne babban dalilin kafa gwamnati.

“Don haka, ya zama wajibi a kan gwamnatoci a dukkan matakai su gyara damararsu sannan su yi kokarin sauke nauyi na al’umma da ya rataya a kansu duk da dai suna da bukatar goyon bayan ‘yan kasa don cim ma nasara.”

Haka nan ya ce, “Abubuwan da ke faruwa na sace-sacen mutane da sauran nau’akan manyan laifuka, sun zama ruwan dare a fadin kasa. Wanda hakan ya haifar da cikas ga harkokin tattalin arzikin kasa da zamantakewa sannan ya dakusar da bunkasar al’umma da ma kasa baki daya.”

A karshe, Makarfi ya jajanta wa ahalin duka wadanda suka rasa rayukansu sakamakon rashin tsaro, haka ma ya tausaya wa wadanda rashin tsaron ya yi sanadin hasarar dukiyoyinsu.

Kana ya jaddada kiransa kan bukatar da ke akwai na ‘yan kasa su bai wa gwamnatoci hadin kan da suke bukata domin karfafa musu gwiwa wajen yin abin da ya kamata.