Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta ce, daga jiya Juma’a za a yanke duka hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara saboda matsalar tsaro.
Hukumar ta ce buƙatar hakan ta taso ne domin bai wa jami’an tsaro damar gudanar da aiknsu yadda ya kamata wajen daƙile matsalolin tsaron da suka addabi jihar.
Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Juma’a mai ɗauke da sa hannun mataimakin shugaban hukumar, Farfesa Umar G. Danbatta.
Da wannan, NCC ta umarci kamfanin sadarwa na Globacom da ya yanke sadarwarsa a faɗin jihar Zamfara, da kuma kashe duk wani kayan aikinsa da ke jihohi maƙwabtan Zamfara wanda barin sa a kunne ka iya taimakawa wajen samun sadarwa a jihar Zamfara.
Hukumar ta ce yanke sadarwar na makonni biyu ne kawai, wato daga 3 zuwa 17 ga Satumban 2021, wanda bayan haka komai zai koma yadda yake.