Matsalar tsaro ta fi ƙarfin Buhari – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana rashin tsaron da ya ke addabar ƙasar a matsayin ‘babbar matsala’ da ta fi ƙarfin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kuma ya ce ya kamata masu ruwa da tsaki su haɗa ƙarfi da ƙarfe, domin magance matsalar.

Tsohon shugaban ya furta kalaman ne a ɗakin karatu na Olusegun Obasanjo Presidential Library da ke Abeokuta a jihar Ogun, yayin da ya ke karɓar Dakta Ugochukwu Williams, ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar PDP da tawagarsa.

Tsohon shugaban ya ce matsalar tsaron ta gagari gwamnatin Muhammadu Buhari. “Idan wani ya zo nan ya ce ina son ganinka, zan amsa ma sa da cewa gani, saboda halin da mu ke ciki a Nijeriya ya fi ƙarfin wani mutum ɗaya ya ce yana da mafita. Na yi imanin sai mun zauna tare kuma mun duba al’amarin tare.”

Jaridar Vanguard ta ruwaito shi yana cewa, “cikin wannan halin babu wanda ke da cikakken tsaro ko a kan hanyar mota, ko a cikin jirgin ƙasa, ko ma a filin jirgin sama. Lallai akwai babbar matsala.

“Ya kamata dukkan ‘yan Nijeriya su sani cewa mun faɗa cikin wata matsalar da ta gagari gwamnati mai-ci, amma bai kamata mu bari matsalar ta fi ƙarfin Nijeriya ba, inji shi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *