Matsalar tsaro ta mayar da Jihar Kaduna shekaru 50 baya – Kudan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a inuwar Jam’iyyar PDP, Hon. Isah Ashiru Kudan, ya bayyana cewa babban abin da zai fi maida hankali a kai idan ya zama Gwamnan Kaduna shi ne magance matsalar tsaro a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ya ƙaddamar da kwamitin kamfen ɗin sa a garin Kaduna, Ashiru ya ce dalilin matsalar rashin tsaro da rarrabuwar kai a Jihar Kaduna ya sa an samu koma baya a wajen cigaba da raya jihar.

”Ina da ƙwarewa a harkar sanin yadda ake hulɗa da jama’a da kuma dabarun samar da zaman lafiya a tsakanin mutane. Idan na zama gwamna abinda zan fi maida hankali akai kenan. Haɗa kan ‘yan jihar mu da kuma kawo cigaba masu ma’ana.

”Jihar Kaduna ta shiga ruɗu, ruɗun da ba za mu zuba ido mu bari shi kenan ta nutse cikin baharmaliya ta halaka ba. Dole mu fantsama mu ceto ta tunda wuri. Wannan shi ne dalilin da ya sa na ke ƙoƙarin ganin mun haɗa kai na zama gwamnan jihar.”

Ashiru ya qara da cewa, “gidan gwamnatin Kaduna kamar na shiga ne In sh Allahu.”

A ƙarshe, Honarabul Ashiru ya gode wa kwamitin kamfen ɗinsa wanda ya ƙaddamar, yana mai cewa ”na kafa kwamiti ne da ya haɗa da dattawa da matasa waɗanda za su riƙa tallata manufar mu, su haɗo mana kan wakilan jam’iyyar mu sannan kuma jama’a domin samun nasara ga abinda muka saka a gaba.