Matsalar Tsaro: Za mu yi wa Shugaba Buhari Kofar Rago – Secure North

Gamayyar wasu kungiyoyi 150, na nan na shirya wata zanga- zangar lumana, akan matsalar tsaro a Arewa.

An dai shirya zanga-zangar lumanar ne, domin ta dace da ranar da shugaba Buhari zai amsa kiran majalisar dokoki ta kasa.

Jaridar Manhaja ta tattauna da biyu daga cikin jagororin wannan zanga-zanga da za a gabatar a kofar shiga ofishin majalisar, sun shaida mana cewa, an shirya ta ne, domin sake matsawa shugaba Buhari ya dau kwararan matakai, akan matsalar tsaro dake addabar arewacin kasar nan.

“Wannan zanga zanga-zanga za ta dau tsawon kwanaki, za mu yi zaman dirshan a kofar majalisa, har sai shugaba Buhari ya zo, sai kuma ya amince da ya biya mana bukatunmu” A cewar Malam I G Wala, daya daga cikin shugabannin zanga-zangar da mu ka tattauna da shi.

Da take amsa tambaya akan wadanne bukatu ne, suke son gwamnatin ta biya musu, a bangaren tsaron, Malama Zainab Marshal ta bayyana cewa “Babbar bukatarmu dai ita ce a inganta tsaro, a kuma sauya shugabannin tsaron kasar nan, sannan a tabbatar an samarwa da jami’an tsaron kayan aiki, da horo mai inganci”

In dai ba a manta ba, kungiyoyi da dama daga arewacin kasar nan, na ta kiraye kiraye ga gwamnatin tarayya, akan lallai ta dau matakin samar da tsaro a wannan yanki, wanda a kullum ke kara tabarbarewa. A makon da ya gabata, Zauren Dattawan Arewa (NEF) ya caccaki gwamnatin tarayya, akan halin ko in kula da take nuna wa matsalar tsaro a Arewa.

Ana dai sa ran sama da mutane 15 ne za su halacci zanga-zangar lumanar ta kwanaki da za a gabatar a ranar talata mai zuwa.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*