Matsalolin Aure A Arewa: Ba mace ce kaɗai ke da ragamar gyara aure ba

Daga AMINA YUSUF ALI

Assalamu alaikum. Sannunku da jimirin karatun Shafin zamantakewa na Blueprint Manhaja. A wannan mako mun zo muku da bayani a kan yadda yawaitar samun matsalolin aure a Arewacin Najeriya wato ƙasar Hausa. Wadda wasu suke ganin ƙasar Hausa a matsayin shalkwatar mace-macen aurarraki a ƙasar nan. Duk da yawan wa’azi da malamai da iyaye suke yi ga mata a kan su bi mazajensu. Da kuma irin izaya da muzgunawa da mata zawarawa suke fuskanta. Wata macen ma tana biyayya ga mijinta har ma a kan abinda a saɓa wa shari’a.

Mace Bahaushiya tun daga ranar da aka haife ta ake mata tarbiyyar yadda za ta zama matar aure ta gari. Tun lokacin girmanta ake nuna mata cewa ba ta da gatan da ya wuce zaman aure. To amma da zarar an yi auren, sai kuma a zo a yi ta samun saɓani wanda idan ba a yi da gaske ba, gayyar ta watse.

To amma ina matsalar take? Anya ba jaki muke rabuwa da shi, mu dinga dukan taiki ba? Anya ko da gaske muke muna son matsalar aure a Arewa ta zama tarihi? Idan da gaske muna so mu kawo ƙarshen matsalar, anya muna bin hanyar da za ta sada mu ga warwarewar matsalar? Waɗannan tambayoyi abin dubawa ne, gaskiya in dai har muna son kawo ƙarshen matsalolin.

Na san wannan rubutu dole zai jawo cece-ku-ce. Amma gaskiyar magana, matsalar a zuciyoyinmu suke. Tun daga kan ma’auratan zuwa kan iyayensu zuwa kan al’umma gabaɗaya. Da za a buɗe zukatan waɗancan mutane, za a ga ba su ba wa aure darajar da ta kamace shi ba.

Wannan matsala ta rashin daraja aure ita ta haifar da matsaloli guda biyu ba su kai uku ba. Na farko akwai matslar yadda ake mantawa da cewa mazajen aure su ma suna buƙatar jagora wajen ganin sun kyautata zamantakewar aure. Abu na biyu kuma, yadda ba a saita zuciyar masu nufin zama ma’aurata a kan ainahin abinda zai faru a gidan aure. Wato zaman haƙuri ne da ibada.

Da farko, idan mai karatu mazaunin wannan yanki ne na ƙasar Hausa, kuma zai lura da yadda harkokin aure suke a yankin, zai ga cewa an ɗora alhakin zaman aure kacokan a kan mace. Wannan ba ƙaramin abin mamaki ba ne. Domin ita mace a cikin alaƙar aure da ma zamantakewar yau da kullum ana ganinta a matsayin ita ce jinsi mai rauni. Kuma wacce aka yarda ko a musulunce tana da ƙaramin hankali musaman idan aka haɗa ta da takwaranta namiji.

Namiji a ƙasar ba a kowanne gida ake yi masa tarbiyya ya zama miji nagari ba. Saboda irin imani da aka yi kowanne namiji an haife shi tsayayye wanda zai iya kula da matan da suke ƙarƙashinsa. Tun daga kan mahaifiyarsa, ƙannensa mata da maza, iyalinsa da sauransu. Ba a tunanin shi ma yana buƙatar a ɗora shi a wata hanya da zai samu wani saiti da zai taimaka masa ya sauke nauyin da aka halitto shi saboda shi. Tunda Allah da kansa ya faɗa a littafinsa mai girma cewa: namiji shi mai tsayawa ne a kan mata. To tunda wanda ya halicce shi da kansa ya faɗi hakan, to me ya sa za mu kau da kai daga jaki mu dinga dukan taiki?

Idan aure ya mutu a wasar Hausa, ba wanda yake cutuwa sama da mace. Amma al’umma ita za su zarga a ce ta qi zaman aure. Haka idan rashin lafiya ta faru a zaman auren. Tamkar al’umma suna mantawa zaman aure na mutum biyu ne. Duk yadda ɗayan ya so a zauna, ɗayan kuma ba ya so ai abun kamar da wuya a samu biyan buƙata.

Idan hatsaniya ta afku a zaman aure, wacce da ma dole ce. Tunda zo mu zauna, zo mu saɓa ne abin. Ba a fiye tsayawa a saurari matsalar mace ba. Kuma ko ta faɗa ma ba za a yarda ba. Wasu iyayen ma kora ta za su yi gidan mijin. Gaskiya kuma hakan ba dai-dai ba ne. Kamata ya yi ko ba za a haɗa su a tare ba, don gudun kada matsalar ta ta’azzara. Ya kamata a ji kowanne ɓangare daban-daban.

Kada a manta, shi ma namijin ɗan’adam ne. Kuma yana kuskure shi ma. Ba dukkan matsalar aure ce laifin matar ba. Shi ma namijin yana laifi. Kuma idan ma bai yi laifin ba, yana buƙatar a tunatar da shi wasu abubuwan da bai sani ba da waɗanda ya sani, kuma ya manta saboda ajizanci.

Shi ma namiji kamata ya yi a dinga yi masa tarbiyya da irin faɗan da ake yi wa mata idan za su shiga gidan aure. Wato shi namiji tamkar an ba shi ‘yancin yin abinda ya ga dama yayin da ita matarsa za a ce ta yi haƙuri a kan dukkan wani hali da mijin zai aikata. Shi kansa namijin ya kamata ya san shi ma yana buƙatar ya yi haƙuri da matarsa. Wacce a zahirin gaskiya ya wuce ta a shekarun haihuwa da ma hankali gabaɗaya. Kuma ya dinga yi mata uzuri. Ba dukan abinda mace ta aikata ne raini ba. Wani abin idan aka yi uzuri da haƙuri aka duba sosai za a tarar ta aikata su ne bisa kuskure na ɗan’adamtaka.

Don haka, ya kamata magabatan namiji da ma malamai masu wa’azi su dinga sanar da shi cewa fa aure ibada ne kuma rashin sauke ɗaya daga haƙƙoƙin matarsa zai iya ruguza tattalin arzikinsa kuma ya tsunduma shi a wuta. Sannan shi ma ya sani kyautata wa matarsa zai iya sanya shi a aljanah. Saɓanin yadda yanzu al’umma har ma da malamai hankalinsu ya fi raja’a a kan su yi wa mata wa’azi su kaɗai. Maza da yawa suna zaluntar iyalansu saboda ba su da ilimin auren ne. Don haka wannan babban ƙalubale ne.

Matsala ta biyu kuma ita ce, yadda ma’aurata suke shiga auren ba tare da sun san meye manufar auren ba. Kuma me za su je su tarar a gidan auren ba. A ƙasar Hausa ana ɗora matasa a kan aure gidan hutu ne ba gidan ibada ba. Su kansu iyayen abinda suka ɗauka kenan. Muatane ƙalilan ne suke ganin gidan aure a matsayin gidan neman aljanna. Shi ya sa sai ka ga an fi fifita namiji mai arziki a kan mai addini idan za a aurar da yarinya. Kuma idan miji yana iya ɗaukar nauyin iyali ta fuskar kuɗi sai ka ga iyaye da ita yarinyar ba su damu da duk wani abu da yake faruwa a gidan ba, ko da yana umartar ta da yin abubuwn da suka saɓa wa addinin Allah.

Shi ma kuma namijin ana nuna masa aure wani waje ne da zai huta da aiki da wahalar Duniya. Idan aka ga namiji yana girki ko shara da kansa, akan ce masa Allah ya kawo aurenka ka huta da wahala. Ka ga an nuna masa aure hutu ne daga wahala maimakon ibada wacce zai samu rabin addininsa a cikinta. Kuma a kaikaice ana nuna masa ita wacce zai auro ɗin baiwarsa ce maimakon abokiyar rayuwarsa da za su yi ibada. Shi ya sa maza da yawa suke ganin mace a matsayin baiwa wacce ba ta da wani amfani sai aikin gida. Wani ko tausayawa da godiya ba ya mata saboda a ganin sa dolenta ta bauta masa daa ‘ya’yansa. Hatta da ɗan hasafi ba ya iya yi mata don yana ganinta matsayin baiwa, ba daɗi, ba ragi.

Sannan shi kansa yanayin da ake shiga gidan auren ma da matsala. Idan saurayi da budurwa za su yi aure, ba su fiye hango ƙalubalen zaman tare ba. Tamkar sun manta faɗar Bahaushe da ya ce, zo mu zauna, zo mu saɓa. Kuma karatun littattafan soyayya da kallon fina-finan Hausa sun yi matuwar tasiri a kan haka. Domin ma’auratan kafin su shiga daga ciki, gani suke yi irin waccan rayuwar da suka ji labari za su tarar a gidan auren. Sai sun shiga kuma, sai a ga ba haka ba ne al’amarin.

Duk da dai akwai soyayya mai ɗimbin yawa a gidajen aure, amma ma’aurata su suke gina ta kafin daga bisani su girbe daɗin da muke gani a zahiri. Sai an yi wa dashen soyayyar ban ruwa tare da zuba masa takin hawuri da kau da kai da kuma yi wa juna uzuri. Uzuri shi ne abu ma fi amfani da yake wara wa dashen soyayya ƙarko, sai kuma addu’a.

To maimakon sabbin ma’aurata su dage a ganin sun gina rayuwrsu yadda za su ji daɗi, sai kuma a koma nuna wa juna ɗanyatsa kowa na ganin baiken ɗan uwansa. Yana ganin shi ne ya canza. Saboda sun tsinci kansu a yadda ba sa zato. Amma da a ce sun shirya wa zukatansu karɓar rayuwar aure a yadda ta zo, walau da daɗi ko ba daɗi da sun huta wa kansu.

Wasu ma sai an rabu da juna an sake aurarraki an ga fa tabbas waccan soyayyar ta fina-finan Hausa da Indiya babu su a zahiri sannan ake haƙura da rayuwar da ta samu. Anan za mu tsaya, Allah ya nuna mana mako mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *