Matsayin dakarun MƊD da aka tsinkaya a Edo – Hedikatwar Tsaro

Daga BASHIR ISAH

Babban Ofishin Tsaro na Ƙasa ya buƙaci jama’a kowa ya kwantar da hankalinsa dangane da motoci da dauran kayayyakin Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gani an girke su a Jihar Edo.

Wani faifan bidiyo da aka yaɗa kwanan nan ya nuna yadda aka tsinkayi kayayyakin na MƊD a Benin, babban birnin Jihar Edo.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata mai ɗauke da da hannun Birgediya Janar Tikir Gusai, Ofishin ya ce ƙasar na ba da gudummawar dakaru ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda na baya-bayan nan shi ne Rundunar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta Abyei (UNISFA), a Kudancin Sudan.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Manjo Janar Benjamin Olufemi Sawyerr ne ke jagorantar tawagar wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta da nata sojojin, amma ta ƙulla yarjejeniya da ƙasashen da ke ba da gudunmawar sojoji don samar da ma’aikatansu da kayan aiki don gudanar da ayyukanta.

Game da bidiyon da aka yaɗa kuwa, “Yana da mubimmanci a bayyana cewa motocin sojojin da sauran kayan aiki masu ɗauke da launin MƊD da aka gani ana jigilarsu ne zuwa tashar jirgin ruwa ta Warri inda za a kwashe su zuwa Sudan ta Kudu don a haɗe su da namu dakarun waɗanda aka ƙaddamar da su cikin UNISFA a watan jiya.

“Hedikwatar Tsaro ƙarƙashin jagorancin Janar Lucky Irabor CFR, na tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewar ƙasarmi ba ta fuskantar kowane barazana da ke buƙatar shigowar dakarun wanzar da zaman lafiya na MƊD,” in ji Hedikatwar.