Matsin tattalin arziki: Gwamnatin Tarayya tana shirin ƙara mafi ƙarancin albashi – Ministan Ƙwadago

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa, tana da shirin ƙarin ma fi ƙarancin albashi daga dubu 30 zuwa sama sakamakon matsin tattalin arzikin da ya addabi Duniya.

Ministan Ƙwadago da ɗaukar aiki na Nijeriya, Dakta Chris Ngige, shi ya bayyana haka a taron bitar al’umma wanda ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta shirya a Abuja.

A cewar Ngige, dole gwamnatin ta duba wannan lamari saboda abinda yake faruwa na yanayin faɗuwar tattalin arziki a Duniya.

Ya ƙara da cewa, wannan karyewar tattalin arzikin ta tava Duniya bakiɗaya. Don haka, Ya ce gwamnatin ta waiwayi dokar mafi ƙarancin albashi don yi mata garambawul. Kuma a cewar sa, gyaran albashin zai fara da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i.

Ya ƙara da cewa, a wannan yanayi da ake ciki, Naira dubu 30 ko kuɗin motar zuwa da dawowa daga wajen aiki ba za ta yi wa ma’aikaci ba.

Daga ƙarshe ya yi kira ga sauran shugabannin ƙungiyoyin ma’aikata da suke ƙarƙashin NLC da su kasance masu bin doka da biyayya ga dokokin da suka shafi aiki a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *