Maulidi: Gwamna Lawal ya buƙaci Musulmi a dage da roƙa wa ƙasa zaman lafiya

Gwamnan Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya yi kira ga al’ummar musulmin jiharsa da ma ƙasa baki ɗaya da a ba da himma wajen roƙa wa Zamfara da ƙasa zaman lafiya.

Ya yi wannan kira ne a cikin saƙon taya musulmi murnar bikin maulidin Fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) da ya miƙa wa al’umma ta hannun kakakinsa, Sulaiman Bala Idris.

A cewar Lawal, “Ina taya Muslmi ganin wannan rana ta 12 ga watan Rabi’ al-Awwal, rana mai albarka wadda a cikinta ne aka haifi Annabi Muhammad (SAW).

“Yau rana ce mai matuƙar muhimmanci inda muke bikin haihuwar Annabi Muhammad (SAW) wanda ya bada rayuwarsa wajen wanzar da ƙauna da zaman lafiya a cikin al’umma.”

Ya ƙara da cewa, kamata ya yi bikin Maulidi ya zama lokacin na koyi da karantarwar Annabi Muhammad wanda a halin rayuwarsa ya nuna kyawawan ɗabi’u ga jama’a hatta maƙiyansa sun amfana da shi.

“Ya kamata mu haɗa kai wajen maido da zaman lafiya jihar ta Zamfara da ƙasarmu Nijeriya. Addu’o’inmu suna da tasirin haifar da sauyi na alheri,” in ji Gwamna Lawal.