Mauludin Majma’u Niass na nuna ƙauna da haɗin kai ne – Shehi Tijjani Auwalu

Mauludin bana, wanda ƙungiyar Majma’u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyas ta shirya, shi ne mauludi karo na 37 wanda ya yi daidai da shekarun Sheikh Ibrahim Niass shekara 123. Gagarumin mauludi ne da ake shirya shi duk shekara don tunawa da Sheikh Ibrahim Niass da gabatar da wasu ayyuka na musamman da tunasarwa ga mabiya ɗariƙar Tijjaniya. A wannan shekarar, za a gabatar da mauludin ne ranar 18 ga Fabrairu, 2023, a Jihar Kebbi idan Allah ya yarda. Don jin taƙaitaccen tarihin wannan mauludin da ƙudirce-ƙudircen da aka tanada da muhimmancin mauludin a wurin al’umma musamman mabiya Ɗariƙar Tijjaniya da Faira, Wakiliyar Blueprint Manhaja, BILKISU YUSUF ALI, ta tattauna da sabon Shugaban Majma’u Ahbab kuma Shugaban qungiyar Tijjaniya Grassa Root Mobilization and Empowerment Innitiative of Nigeria (TIGMEIN) kuma jika ga Sheikh Ibrahim Inyas, wato Shehi Tijjani Sheikh Sani Auwalu, inda ya yi qarin haske kan wannan muhimmin taro na mauludi.

Yaushe aka fara wannan mauludin?

An fara gudanar da wannan mauludin a shekarar 1986 shekara 37 da suka wuce.

Su wa ye suka assasa Mauludin?

‘Yan’uwa almajiran Sheikh Ibrahim Niass ne suka assasa wannan mauludi ƙarƙashin jagorancin marigayi Sidi Ahmad Kulaha wanda ya zama mataimakin shugaba da Sheikh Dahiru Abubakar Kurmi Shugaba, An fara da haɗuwa a yi karatun Alƙur’ani duk Lahadi anan ofishin Sidi Ahmad Kaulaha da ke Lagos duk Lahadi. Yayin da ake yin wannan karatun sai wani ɗan’uwa ya zo ya gansu ya tambayi su “wannan me suke yi” suka ce “karatun Al-ƙur’ani suke yi hadiyya ga Sheikh Ibrahim Inyas”. Sai ya ce “antu ma majma’u Ahbab”. Daga nan ne ma wannan suna ya fito. Daga nan aka samu mutane haziƙai ƙarƙashin jagorancin Alhaji Garba Hamza da Sheikh Ɗahiru Abubakar da Alhaji Talle da Alhaji Sani Rogo da Sheikh Aliyul Gali da Alhaji Aminu da saura da yawa suka ƙara ƙaimi da rungumar a’amarin . Daga nan aka yi shawara a fara zaman mauludi. An fara wannan mauludi a Lagos duk shekara, tun ana yi a gida har aka fara yi a waje daga nan aka ci gaba da yi a babban waje , sai aka fara yi a wajen jihar Lagos. A shekarar 1991 an yi a jihar Kaduna sai 1992 a Ibadan. A 1993 an yi a Kano. 1994 an kai mauludin Ilorin, 1995 aka yi a Sakkwato. A shekarar 1996 aka je Osun 1997 aka je Filato haka dai aka yi ta tafiya ana zagayawa har shekaru huɗu baya aka yi a Bauchi da jigawa da Sakkwato. Shekarar 2022 an yi a Zamfara Bana za a yi a birni Kebbi in Allah ya yarda.

Ya ya ka ke ganin cigaban Mauludin.

Gaskiya wannan ƙungiya ta yi matuƙar albarka an samu cigaba a al’amuranta, duba da tun da aka fara ba a daina ba, kullum cigaba a ke samu qara haɓaka mauludin yake yi, ƙara tagomashi yake yi , mutane ƙara himmar hakar suke yi, Babu wani taro kowanne iri ne a ƙasar nan da yake tara jama’a kamar mauludin Shehu wannan ba ƙaramar nasara ce ba. Kuma Alhamdlillahi, tunda ake yin mauludin babu wani abu na ɓatanci ko assha ko rashin jin daɗi da ya taɓa biyo bayan mauludin sai ma na san barka. Wannan ba ƙaramar albarka ce ba. Taron da aka fara a ɗaki da karatun Alƙur’ani yau ana yinsa a jihohi wannan albarkace ta Shehu Ibrahim Kuma albarka ce ta almajiran Shehu Ibrahim. Wannan ƙungiya ta yi matuƙar albarka Sheikh Abdullahi Inyas ya sa mata hannu ya sa mata tambari kuma ya sa hannu ya ba da izini akan mazaje jajirtattu irin su Sheikh Ɗahiru Abubakar da suka tsayawa ƙungiyar , wanda yake shugabantarta tun a wannan shekarun har zuwa shekarar 2022 da Allah ya yi masa rasuwa. Allah ya saka masa da Alheri shi da Sidi Kaulaha, Amin.

Mai ya bambanta Wannan mauludin da sauran mauludai na Shehu da ake gudanarwa?

Wannan mauludi na musamman ne, wanda ya haɗa kowanne ɓangare, kowanne ɗan zawiyya kowanne gidan Shehi duk an haɗu a inuwa guda. Kowanne Shehi yana zuwa wannan mauludi kuma in an zo mauludin kowa yana jin wannan maulidn nashi ne babu wariya.

Me ka ke ganin ya janyo wannan nasarar?

Wannan nasarar tana ɗamfare da ƙarfin almajiran Shehi Ibrahim Inyas da yawansu da iya tara jama’a da haɗin kansu da soyayyarsu da iya mu’amalarsu shi ne silar wannan nasarar. Goyon bayan da manyan Shehunnanmu suke bayarwa shi ma nasara ne. Don kuwa, duka taron almajiran waɗannan shehunnan ne da masoya ke zuwa. Haɗin kai shi ma yana cikin ƙashin bayan nasarar wannna taron da ake yin a mauludi. Taro ne da ke kawo cigaban al’umma, ba ma iya ‘yan ɗariƙar Tijjaniya ba. Sannan ‘ya’yan Shehu suna zuwa wannan taro tun zamanin Shehu Abdullahi tun ana zuwa mutum goma, ishirin, akwai shekarar da ta zo sai da muka zo da mutum tamanin da wani abun daga Kaulaha. Kuma duk shekara ne ‘ya’yan Shehu Ibrahim da jikoki da muƙaddamai da almajiran Shehu suna tasowa daga Sinigal su zo. Gwamnati tana samun damar ɗaukar wannan taro a mafi yawan lokuta saboda kwadayin samun wannan albarka da Shehu Ibrahim don haka suke ba da gudummawa.

A ƙarshe me ne fatanka

To Alhamdililah fatana a yi taro lafya a kammala lafiya a samu falalar da ake samu ta zumumci da tausayi da taimakon juna da ƙara jin wasu halaye na Sheikh Ibrahim Inyas da kuma fatan a yi aiki da duk abin da aka ji. Sai kuma addu’a ta musamman ga Sheikh Dahiru Abubakar da amininsa Sidi Kaulaha sun riqe ƙungiyar na tsahon shekara 37 kuma Allah ya yi musu rasuwa duka kusan lokaci ɗaya tsakaninsu bai fi kwana 40 ba. Wannan shi ne mauludi na farko da za a yi a birnin Kebbi ba tare da su ba. Muna addu’ar Allah ya jikansu da gafara mu kuma Allah ya shige mana gaba a cikin wannan aiki.
Na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *