MAVIN ta buƙaci a daina nuna wariya ga masu nakasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A yayin da ake gudanar da bikin zagayowar ranar nakasassu, ƙungiyar Musulmi Masu Nakasassu ta Nijeriya (MAVIN) ta buƙaci zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu da zaɓaɓɓun gwamnoni da su samar da ayyukan yi ga nakasassu a faɗin tarayyar ƙasar nan.

A cikin wata sanarwa, shugaban ƙungiyar, AbdulWasi Salaudeen, ya ce nakasassun Nijeriya sun cancanci a yi bikin.

Ya baygana cewa, duk da rashin daidaito, har yanzu nakasassu su na cika sashinsu na ayyuka daban-daban.

Ya ƙara da cewa, “Dukkanmu mun cancanci yabo domin mun yi nasarar tattara kanmu waje guda, lokacin da kuma bayan zaɓe cikin lumana, kwanciyar hankali da riƙon amana, tare da mutunta ƙabilunmu daban-daban, bambancin addini da kuma bambancin siyasa.

“Mun yi imanin cewa, nan da wani lokaci za mu shawo kan ƙananan ƙalubalen da muka gani a matsayin faɗowar babban zaɓe, kuma za mu ƙara ƙarfi da haɗa kai a matsayinmu na al’umma zuwa babbar ƙasa da muke fata.

“MAVINS na taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da sauran waɗanda suka yi nasarar zaɓe a faɗin ƙasar murna. Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba mu ƙara da cewa nasarar da kuka samu a zaɓen bai kamata ta kowace hanya a yi wasa da ita ba, a’a, a riƙa kallon ku a matsayin wani nauyi da masu zaɓe suka ɗora muku.”

“Haƙƙin ya rataya ne a kan ku da ku mayar da wannan karimcin mai kima, ta yadda ba wai kawai ku kasance masu girman kai a cikin nasara ba, har ma da yin aiki da nauyin da ke kan ofisoshin ku, don tabbatar da wa’adin da aka ba ku.

“Yayin da kuke shirin rantsar da ku nan gaba a cikin wata, muna so mu roqe ku da ku naɗe hannun riga kafin manyan ayyukan da ke jiranku. ’Yan Nijeriya na fatan samun shugabanci mai manufa da manufa wanda zai dace da kalmomi da ayyuka, da kuma fassara alƙawuran zuwa wadatar tattalin arziki da samar da kyakkyawar sauyi a cikin al’umma domin amfanin talakawa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *