Mawaƙan Annabi suna rayuwa ne a gaɓa mai haɗari, inji Mahmoud Nagudu

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Mahmoud Isma’il Ibrahim, wanda aka fi sani da Mahmoud Nagudu, fitaccen mawaƙi ne a fagen yabon Manzon Allah (SAW) tun yana ƙaramin yaro, sai dai ya yi fice ne a fagen waƙoƙin fim a shekarun baya. Amma dai yanzu ya daɗe ba a jin ɗuriyarsa a fagen waƙoƙin Nanaye, sai na yabon Manzon Allah kaɗai. Kasancewarsa mai ilimi a fagen yabon, ya sa Wakilin Manhaja a Kano, Mukhtar Yakubu, ya nemi tattaunawa da shi a kan abubuwan da yabon ya ƙunsa a fage na ilimin musamman ganin yadda a ke tafiyar da tsarin kara-zube a wannan lokacin. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda ta kasance:

MANHAJA: Mahmoud Nagudu, da ya ke a yanzu ka mayar da hankalinka wajen waƙoƙi na yabon Manzon Allah (SAW), za mu so ka yi wa masu karatunmu bayani a kan abin da waƙoƙin suke a fage na ilimi?
MAHMOUD NAGUDU: To idan aka ce a na son a yi magana a kan yabon Annabi S A W, to farkon abin da za a fara ɗauka bisa al’adar Bahaushe, menene yabon shi kansa ba sai na Manzon Allah ba. To yabo dai shi ne ambaton halaye da ɗabi’u na ɗan Adam domin ya yi ma sa daɗi a zuciyarsa shi wanda aka yi wa yabon ko kuma wanda yake ƙaunar sa, to wannan shi ne a ke nufi da yabo. To idan aka zo na Annabi S A W, wanda shi ne mafi girman halittar Allah, wanda idan ka yabe shi, tabbas duk abin da ka faɗa, to ba ka iya faɗar yadda Allah ya tsara shi ba, ka taƙaita wani abu, don haka a na yin yabon Manzon Allah ne a faɗi kyawawan halayen sa da mu’amalar sa, saboda yana cewa “an aiko ni don na koyar da kyawawan ɗabi’u.” To duk wanda yake so ya samu kyakyawar ɗabi’a sai ya yi koyi da shi, to shi kuma mai yabo sai ya faɗi kyawawan ɗabi’un. To, sai kuma zambo wanda shi ne a yi wa wanda aka san yana jayayya da Annabi, yana ƙin sa, yana hassada ga Annabi na kusa da na nesa. Abin nufi na can lokacin Annabi da waɗanda suke a wannan lokacin, duk sai an yi zambo a kan su an fifita Annabi a nuna a duniya Allah bai yi halittar da ta kai Annabi ba. Duk wanda ka ga ya yi daraja a duniya kowaye to sai ya ravi Annabi yake daraja, amma da ka yi nesa sai ka ga darajar ka ta watse. To, waɗannan abubuwan mai waƙa zai yi riƙo da su ya faɗi halayen Annabi. Misali; gaskiya, adalci, rangwame, da kuma jure wautar wawaye. Don ka ga ba a taɓa yin wanda ya kai girman sa a wajen Allah ba, amma sai a yi ma sa abu wanda a ke tunanin in ni ko kai aka yi wa ba za mu haƙura ba, amma shi sai ya haƙura, sannan kuma ya zauna da mutanen da ya san wane masoyi na ne, wane maƙiyi na ne, kai har wanda ma ba Musulmi ba za su zo su zauna da Manzon Allah duk kyaun ɗabi’un sa ne yake sa su musulunta. Amma mu a yanzu Musulmi, idan ka zo ka kalle mu in dai ɗabi’un mu ne, ai ba za ma a samu wani ya shiga Muslunci ba. Kuma shi yabon Annabi yana yi wa har dabbobi daɗi, don akwai wanda yake jan raƙumin Manzon Allah yana yabon Annabi har Manzon yake cewa, ka tafi da mu a hankali, saboda idan yana yin baitukan waƙa, shi kansa raƙumin da Annabi yake kai sauya tafiya yake yi. Imamul Busuri yana cewa “Allah ya yi ta salati ga Annabi matuƙar ciyayi su na motsi.” A na yabo a na farantawa raƙumi zuciya,” To, idan har an yabi Manzo an faranta wa raƙumi zuciya, Ina kuma ga mutum. To wannan shi ne gundarin abin da ya sa a ke yin yabon Annabi da kuma ma’anar yabon.

Amma da yawa masu yabon a yanzu ba su san abin da ya kamata su yi ba a wajen yabon kamar yadda ka yi bayani kenan?
Wato yabon Annabi (SAW) mai yin sa gaskiya yana da falala, amma yana rayuwa a wani waje na haɗari. Saboda idan ya faɗi kalma duk ƙanƙantar ta wadda yabo ne amma ta taɓa matsayin Manzon Allah, to Allah ba ya yin afuwa ga mutanen da su ka taɓa Annabi. Don haka shi mai yabo abin da a ke so ya je ya zauna ya yi nazarin, ya duba waɗanne gwala-gwalain kalmomi ne ya tara da yawa, kalmomin da ba a tava faɗa wa wani ba. In ka ji an taɓa yabon wani sarki ko hakimi ko wani Alhaji, to kar ka faɗa wa Annabi wannan saboda shi ya wuce duk in da za ka faɗe shi. Don haka yabon Annabi, in ka na son ka zauna lafiya shi ne dukkan abin da ka san shi ne ƙarshe a iya tunanin ka, to shi za ka faɗa wa Annabi, in dai har Annabi ba a ce masa Allah ba, wato shi bawan Allah ne, to duk abin da yake muƙami ne, kuma yake a ƙasan Allah to Annabi ya fi wannan daraja, don shi ba Allah ba ne, amma ya fi dukkan halittun Allah daraja. Annabi S A W, bawa ne na Allah, amma shi ne shugaban halittar Allah, to ka ga me za ka faɗa ka faɗi falalar sa, to a nan ma za ka iya satar amsa ka je ka binciki yadda aka yabe shi. Misali; tun daga iyayen sa, in mu ka ɗakko farkon yabon za mu ga Allah ya yi ta yabon Annabi a cikin Attaura, Zabura, Injila, ka ga tun Annabi bai bayyana a duniya ba. Sannan farkon abin da aka fara yabon sa da shi a duniya shi ne, abin da aka faɗa wa mahaifiyar sa ta sanar da shi. “Ki ce Ina neman tsarin Allah ya kiyaye mini wannan ɗa na wa, Allah wanda yake shi guda ɗaya, ya kiyaye mini daga dukkan hassada kuma ki ambace shi Muhammadu.” Wato abin yabo, ka ga an fara yabo kenan. Haka Sayyidina Abbas R.A. ya yi ta yabon Manzo yana bada labarin yadda hasken Manzon Allah ya yi ta tahowa tun daga Annabi Adamu har zuwa Annabi Ibrahim A.S. zuwa ga Manzon Allah yana kiyaye wannan hasken, to wannan ya sa dole mai yabo, sai dai ya yi yabon da aka tava yin irin sa, kada ya ɗauka yanzu ya ƙirƙiro wasu sababbin abubuwa wai shi burgewa yake yi, a’a waɗanda suka san Annabi su ne su ka san Annabi, kawai kwafa mu ke yi, kada ka je ka zaƙe kada ka je wajen ka faɗo wata kalma ga Annabi, Allah ya yi fushi da kai, domin mutum zai iya furta wata kalma guda ɗaya wadda bai san girman ta a wajen Allah ba, amma sai Allah ya yi ma sa rahama saboda da ita duk abin da zai yi bayan wannan ya zama rahamar Allah tana tare da shi. Ko mutum ya furta wata kalma wadda bai san girman ta ba a wajen Allah, sai kalmar ta zamo an yi nesa da shi daga rahamar Allah, ya zamo cikin azabar Allah, har lokacin da babu iyaka, kuma Allah ba zai ƙara kallon wannan mutum da rahama ba.

Idan na fahimce ka, wato ganganci ne mutum ya fara yabon Manzon Allah ba tare da ilimi ba?
To, ai babu ma abin da ya kai hakan ganganci domin shi ne ganganci mafi girma, domin wajibi ne abin da za ka yaba ka san shi, duk da dai cewa babu wanda ya isa ya san Manzon Allah sai Allah. Amma abin da a ke nufi shi ne, ka san shi ka san irin fagen da aka ware wanda ba a shiga wannan hurumin. Misali; akwai waɗanda malamai ne, amma su kan fassara ayoyin Alƙur’ani bisa ƙwaƙwalwarsu da tunanin su ga yaren Larabci. In dai ka ji Allah ya faɗa wa Annabi magana, wadda ka ji a zuciyar ka me ya sa Allah zai faɗa masa haka, to fa yabo ne a wajen Annabi. Misali, idan ka ɗauki ayar “Wa wa jadaka dallan fahada.” Idan ka fassara ta a yadda wawayen malamai suke fassara ta, to fa ka tashi daga aiki, don Annabi Allah bai taɓa zargin sa ba, bai tava cewa ya yi laifi ba, yabon sa yake yi, don haka sai ka gane ka san abin da za ka yaba. In ba ka sani ba ka yi ɓarna, to fa ka tashi daga aiki, don haka Annabi wajibi ne mutum ya tashi ya je makaranta ya san shi a ilimi, in ba haka ba, sai mutum ya jefa kan sa a wani ramin da ba zai fita ba.

Akwai wani abu da mawaƙa a yanzu suka shahara da shi na cewar, sun yi mafarki da Manzon Allah (SAW), wanda hakan ya sa a ke ganin kamar wasa ne da darajar Annabi. Me za ka ce kan hakan?
Wato shi mafarkin Annabi, mafarki ne na gaskiya, domin ya faɗa cewar, “wanda ya gan ni a mafarki, to ni ne. Shaiɗan ba ya kama da ni.” To, matsalar ita ce, mafarki da Manzon Allah yana da matsaya da yawa. Shin Annabi da ka yi mafarkin nan cewa ya yi ka zo ka faɗa? Kuma abin da ka gani ko aka faɗa ma ka a mafarkin, idan ka faɗa ya mutane za su kalli abin? Sayyidina Aliyu (RA) yana cewa, “yana ɗaya daga cikin jahilci ka faɗa wa mutune abin da ba daidai da hankalinsu ba.” Yanzu Misali, sai ka ce ka yi mafarki da Annabi, ya ce ma ka kaza ko ya yi kaza a gaban ka, to idan wani ya ƙaryata, ya ji Annabi bai kai wannan matsayin ba to ya hallaka, to idan ya tashi hallaka har da kai, domin kai ka zuga shi har ya yi shakka cikin abin da bai sani ba. Don haka wajibi ne mu daina yaɗa abu ko da na gaskiya ne wanda zai kawo wasu shakka da matsayin Annabi. Ina ɗaya daga cikin waɗanda suka yi imamin a na iya ganin Annabi a mafarki ko a zahiri, saboda mu Annabi ya faɗa mana wanda ya ganni a mafarki, da sannu zai ganni a fili, don haka ko a fili aka ce an gan shi to na yarda, don ni ban san abin da ya kai shi girma ba, Amma duk wanda ya yi, to ya rufa wa kan sa asiri abin da ku ka yi na son Annabi har ku ka gan shi to ku dage ba sai kun faɗa wa kowa ba, don kar ku zama abin da ku ke yi ya jawo muku girman kai ku daina tallan son Annabi ku dawo ku na tallan kan ku, idan ya zamo ka na tallan son Annabi, amma ta wayo ka na tallan kan ka ne to fa ka tashi daga aiki. Don haka duk wanda yake yabon Annabi, to ya bi Annabi da gaske, ba ya ɗauka cewar yabon Annabi wata hanya ce da zai yi wayo ba, don ya rinƙa biyan buƙatar sa. Kada ka zama ka na nuna wata da ɗan yatsan ka, amma ba watan ka ke nunawa ba kai ka ke so a kalla, don haka duk wanda ya zo yana yabon Annabi dole ya zama Annabin yake nufi ba shi kan sa yake son a gane shi ne ya ke yabon Annabi ba, don duk abin da ka rava a duniya, ko .enene ba za ka samu ɗaukaka ba kamar Annabi, shi kaɗai ne idan aka raɓe shi za a ɗaukaka, kuma daga an rabu da shi to an hallaka, don haka duk mai yin yabo abin da ya kamata ya zama Annabin ne a gaban sa, sannan kada mu faɗa wa Annabi kalmomin da idan an zo an tambaye mu a lahira ba mu san amsarsu ba.

Madalla, mun gode.
Ni ma na gode sosai.