Mawaƙi Ado Gwanja zai angonce yau Juma’a

Daga AISHA ASAS

An kwana biyu ana raɗe-raɗen shahararren mawaƙin mata, Ado Gwanja, zai yi sabon aure bayan rabuwarsa da matarsa ta farko wadda suke da ‘ya ɗaya tilo da ita, sai dai babu wata hujja da ke nuna gaskiyar zancen, wanda hakan ke sa lokacin ya zo ya wuce ba tare da an ji labarin ɗaura auren ba.

Sai dai a wannan karon labarin ya bambanta, domin ya samu isnadi mai ƙarfi da za a iya cewa ƙamshin gaskiyarsa ya rinjaye warin ƙaryarsa, domin labarin ya fito ne daga bakin yayan mawaƙin Alhaji Sa’idu Gwanjo, wanda ya sanar da ɗaurin auren a ranar Juma’a 21 ga watan Yuli, 2023, a zauren ɗin masu yin fim na MOPPAN Associates, kamar yadda Mujallar Fim ta wallafa.

Ɗaurin auren wanda za a yi a Masallacin Juma’a da ke cikin Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano zai kasance shekaru biyu bayan rabuwar auren mawaƙin da matarsa ta farko Maimunatu, mahaifiyar ‘yarsa Asiya, wadda ake kira da Balaraba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *