Mawaƙi M. Shareef ya zama Ambasadan gidan talabijin na Qausain TV

Daga WAKILINMU

Sabon gidan talabijin na Qausain ya naɗa shahararren mawaƙi Umar M. Shareef a matsayin jakadansa na farko a Kaduna.

Babban Shugaban Kamfanin Qausain Group, Alhaji Nasir Musa Idris (Albani Agege) ne ya bayyana haka a yayin ƙaddamarwar wanda gidan talabijin ɗin ya shirya a harabar ofishinsa da ke Sultan Road, GRA Kaduna a wannan makon.

Shugaban kamfanin ya bayyana jin daɗinsa tare da kuma miƙa godiyarsa ga Allah SWT da kuma ilahirin ma’aikata da waɗanda suka bada gudumuwa har wannan gidan talabijin ya tabbata.

Malam Nasir ya bada tabbacin cewa gidan talabijin ɗin zai ta fi daidai da zamani kamar sauran manyan didajen talabijin na duniya, tare da kare dukkan wani haƙƙin da ya rataya a wuyansu na ganin sun samar da ingantattun bayanai da nagartaccen ilmantarwa domin amfanin al’umma bakiɗaya.

Shi ma a nasa jawabin Babban Daraktan Qausain, Alhaji Musa H. Isa, ya bayyana cewa sun samar da tashar Qausain TV ne daidai da zamani da kuma bin duk wasu ƙa’idoji na samar da ingantaccen gidan Talabijin.

Musa H Isa, ya kuma gabatar da fitattacen mawaƙi Umar M. Shareef a matsayin jakadan tashar ta Qausain TV. Inda shi ma mawaƙin ya bayyana jin daɗinsa tare da alƙawarin kawo cigaba mai ɗorewa a matsayinsa na jakadan tashar.

Tun da farko a tsokacinsa, Babban Manajan tashar, Umar Faruk Adam ya nemi goyon baya daga al’umma da ganin sun mara wa tashar baya ta fuskar ƙarfafa gwiwa da kuma kawo tallace-tallace.

Ya kuma ƙara da cewa sun samar da hanya mai sauƙi ga masu sha’awar sanya hannun jari ko son ƙulla alaƙar kasuwanci da Gidan Talabijin ɗin na Qausain TV.