Mawaƙiya Tina Turner ta kwanta dama

Daga AISHA ASAS

Fitacciya kuma shahararriyar mawaƙiyar Tina Turner, wadda ta kafa tarihi a duniyar waƙa ta mutu tana da shekara 83.

Mawaƙiyar, wadda aka haifa a Tennessee da ke Amurka, ta rera waƙoƙi da dama kamar, ‘Mountain High’, ‘What’s Love Got to Do With It’, ‘River Deep’ da dai sauransu.

Za mu iya cewa, matsalolin rayuwar aure da mawaƙiyar ta fuskata ne suka zama sanadin ɗaukakar ta, domin kamar yadda aka tabbatar kusan duk waƙoƙin da ta ke rerawa na ɗauke da kukan zuci na daga rashin jin daɗin zamantakewarta da tsohon mijinta mai suna IkeTurner.

Turner daɗaɗɗiyar mawaƙiya ce da ta fara samun shuhura tun a shekarun 1980, sannan ta kwashe sama da shekaru 60 a harkar waƙa. Hakazalika, ta lashe kyaututtukan Grammys har sau 12.

Tabbas za a jima ba a iya mantawa da mawaƙiya Tina Turner ba, duba da yadda mutuwar ta girgiza duniyar mawaƙan duniya.