Maza ba su cika kai ƙara kotu a kan cin zarafin da matansu ke musu ba – Barista Mariya

“Mata su dinga neman haƙƙinsu a kotu kan cin zarafinsu”

“Lauyoyi mata na ba wa mata gudunmawa mai yawa a karu”

“Mu na bayar da gudunmawa wajen kare haƙƙin mata ba tare da karɓar kuɗi ba”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Aikin lauya aiki ne na kare haƙƙoƙin jama’a a gaban shari’a, don ƙwatowa mai haƙƙi haƙƙinsa da tabbatar da ganin an yi wa wanda aka zalunta adalci, an kuma hukunta wanda ya yi ba daidai ba. Ga duk ma’aboci bibiyar yadda ake gudanar da shari’a ko ganin yadda lauyoyi ke muhawara da bincike don kare wanda suke wakilta, ya san cewa, aikin ba ƙarami ba ne, aiki ne da ke buƙatar jajircewa, nuna rashin tsoro da kuma dagewa a kan gaskiya. Waɗannan halaye da ake buƙata a wajen tsayayyen lauya mai nagarta ba kasafai ake samun su a wajen mutum ɗaya ba, ko da kuwa namiji ne, ballantana lauya mace. Barista Mariya Mohammed Shittu, mace ce mai maganin maza. Tsayayyiya a kan gaskiya, mai ilimi da juriya a aikin da ta sa a gaba kuma ta ke kishin sadaukar da lokacinta da duk abin da ta mallaka, domin kare wanda aka zalunta ko tauyewa haqqi, musamman mata waɗanda ke fuskantar danniya da ƙuntatawa daga wasu azzaluman mazaje. Wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu, ya samu ganawa da Barista Mariya Shittu, masaniyar shari’a, ýar gwagwarmayar kare haƙƙoƙin raunana, da kare ýancin mata. Za ku ji yadda wannan jajirtacciyar lauya ta fara samun sha’awar shiga wannan aiki mai martaba.

BLUEPRINT MANHAJA: Zan so ki gabatar mana da kanki?
BARISTA MARIYA: sunana Barista Mariya Mohammed Shittu. Ni lauya ce mai zaman kanta, mai aikin kare haƙƙoƙin jama’a, kuma uwa mai kula da tarbiyya.

Ba mu taƙaitaccen tarihin rayuwarki?
An haifeni a Jihar Adamawa, a ƙaramar Hukumar Numan a shekarar 1980. Nice ƴa ta farko a gidanmu. Na fara karatuna na firamare a Gombe, sannan na yi sakandire na a Makarantar Sakandiren Gwamnati ta ‘Yan Mata wato GGSS Yola a Jihar Adamawa, inda na kammala a shekarar 1997. Daga nan na samu shiga Kwalejin Nazarin Aikin Shari’a da Ilimin Addinin Musulunci wato College for Legal and Islamic Studies. Wannan shine ginshiqin zama na lauya.

Na tuno lokacin da mahaifina Allah Ya yi masa rahma ya so na je Kwalejin Horar da Malamai, domin in zama malamar makaranta, amma na dage a kan ni Legal na ke so in je. Haka tafiyar ta fara.


Daga nan na samu gurbin karatu a Jami’ar Maiduguri a shekarar 2000 inda na karanci ilimin Shari’a, har kuma na samu nasarar wucewa makarantar samun ƙwarewa kan aikin shari’a wato Nigerian Law School da ke Abuja. An rantsar da ni a matsayin cikakkiyar lauya a shekara ta 2008. Wannan shine ya bani damar zama lauya mai iya kare haƙƙin jama’a a kowacce kotu a Nijeriya.

Mai ya ja hankalinki ki ka shiga aikin lauya?
E, zan iya cewa hakan wani sauyin tunani ne ko ra’ayi na samu daga abin da naso tun da farko, domin da naso ne na zama Likita.To, sai dai a lokacin da na kammala jarrabawar ƙaramar sakandire sai ban samu shiga ɓangaren kimiyya ba, sai na tafi ɓangaren fasaha wato Art, daga nan sai na tsinci kaina da sha’awar zama lauya. Saboda a lokacin akwai wani abokin mahaifina shi ma lauya ne, (Allah Ya jiqan sa da rahama), ya taɓa kawo ajiyar rigar su ta lauyoyi gidanmu sai wata rana na gwada, daga nan sai raina ya qara biyawa da zama lauya, musamman idan na ji yadda yake bayar da labarin shari’a sai abin ya ƙayatar da ni, na ji Ina daɗa son zama lauya.

Za ki iya tuna shigar ki kotu ta farko, wacce kara ki ka gabatar ko ki ka kare?
Shigata kotu ta farko shine wata ƙara da na je a ƙarƙashin ƙungiyar matan lauyoyi ta Fida a Babbar Kotun Yanki ta Upper Area Court 1 da ke Kasuwar Nama a Jos, kuma ƙarar ta shafi rikicin aure ne, amma daga baya muka sasanta ba a yi zaman kotu ba.

Yaya ki ke ganin gudunmawar da mata ke bayarwa a ɓangaren shari’a?
Gaskiya mata suna bada gudunmawa matuqa, musamman a game da ƙararrakin da suka shafi rikicin aure ko cin zarafin mata. Kuma haƙiƙa suna nuna jarumta da jajircewa tare da ƙwarewa wajen ganin cewa, sun kare wanda suke wakilta ko da kuwa babu ko sisi. Mata suna tsayawa da zuciya ɗaya ba son rai don ganin an yi adalci.

Wanne ƙalubale ki ka fuskanta a baya cikin wannan aikin da kuma yadda ya ba ki ƙwarin gwiwa na ci gaba da gwagwarmaya?
Gaskiya akwai ƙalubale masu yawa a harkar shari’a, musamman idan ƙara akwai sarƙaƙiya, ko kuma idan ka samu abokin hamayya da ke da aƙidar lallai sai ya yi nasara ko ta halin ƙaƙa.Wata rana idan wani abu ya faru na kan ji kamar na bar aikin kwata kwata ma, sai na ke ganin yaushe zan yi nasara ne? Yaushe zan ƙware nima?

A hankali kuma wata rana sai a samu nasarar, sai kuma na samu mutane suna ƙarfafa min gwiwa, musamman mai gidana wanda shi ma lauya ne, shi yake koyar da ni abubuwa da dama, kuma ya warware min abin da ya shige min duhu. To, waɗannan su ne abubuwan da suke ƙarfafa min gwiwa na ci gaba da gwagwarmaya, musamman wajen kare haƙƙoƙin mata da yara da aka ci wa zarafi.

A matsayinki ta mamba a ƙungiyar lauyoyi mata ta FIDA, wacce gudunmawa ku ke bayarwa wajen kare haƙƙoƙin mata da yara?
Muna bayar da gudummawa wajen kare haƙƙoƙin mata ba tare da karvar ko sisi ba, wato abin da ake cewa “Pro Bono services”. Tunda dama ƙungiyar mu ƙungiya ce da ke zaman kanta, da bata wariya don addini, ko al’ada. Ƙungiya ce da ta ƙunshi mata lauyoyi ƙwararru da suke rajin kare haƙƙin mata da yara, wanda kuma shi ne ginshiƙin kafa wannan ƙungiya. Kuma manufarta ita ce, kare mata marasa ƙarfi da gajiyayyu da kuma yara. Muna bada ƙwarewarmu sosai ganin mun ƙwatar wa mata ƴanci.

Game da ƙorafe-ƙorafe da ku ke karɓa na mata, shin wanne ɓangare ne aka fi kawo ƙara a kansa?
Gaskiya ƙorafe-ƙorafe da muka fi karɓa shine, damuwoyi tsakanin ma’aurata, rashin ciyarwa ko kula da haƙƙoƙin iyali da kuma cin zarafi ga mata. Kamar duka da kuma fyaɗe musamman ga yara ƙanana.

Shin kin gamsu da yadda dokokin Nijeriya suke hukunta masu laifi, musamman a ɓangaren cin zarafin mata?
Gaskiya, duk da mu na da dokoki da yawa a Nijeriya da suke hukunta masu cin zarafin mata. Misali inda ake samun tsaiko shine, gurin da doka ta bar wa Alƙali ragamar hukunta mai laifi bisa ga ra’ayinsa wato abin da a turance ake cewa, “at the discretion of the court”. Na biyu kuma shine, amfani da kalmar “shall” da “may” inda shall ke nuna cewa, dole sai abin da doka ta ce za a yi amfani da shi wajen hukunta wanda ya ci zarafin mace.

Misali a hukuncin fyaɗe an tanadar da shekara 21 ko zaman waƙafi, wato ‘life imprisonment’ kamar a dokar Jihar Filato ta Penal Code, sashi na 256 zuwa 257, amma abin rashin daɗin shi ne, an bar wa alkali zaɓi. Shi ya sa sai ka ga da wuya ake samu a hukunta masu laifukan kamar yadda ya kamata. Hakan kuma ke sa wasu su cigaba da aikata wannan cin zarafin ga wasu matan.

Wacce shawara za ki bai wa mata da ke rayuwa cikin ƙunci a gidajen auren su, don su nemawa kansu ýanci a vangaren shari’a?
Shawarwari da zan bai wa mata shine, kada su yi shiru ko su ɓoye cin zarafi, saboda cin zarafi abu ne mai girma a shari’a, tunda dokar lasa ta bai wa kowanne ɗan ƙasa ‘yanci don yin walwala da kuma yin addini, ba tare da tsangwama ko don jinsi, ko addini, ko bambanci na ra’ayi ba, kamar yadda yake a sashi na 32 zuwa na 42. A bisa haka ne na ke kira ga mata su fito su faɗa duk lokacin da aka ci zarafinsu ta kowacce fuska wato a zahirance (misali duka ko fyaɗe) sai kuma na baɗini (wato psychological violence) Su kai rahoto ga qungiyoyin da aka tanadar don amsa irin waɗannan koke koke, domin samun mafita.

Shin kin taɓa karɓar wani koke inda mace ta ci zarafin namiji, amma ya kasa kai kuka gaban kotu?
E, gaskiya su ma maza akan ci zarafin su, domin cin zarafi ba wai sai duka ba. Mace ta hana miji kwanciyar hankali, ko kuma sanya mishi wasu ƙa’idoji da ba ra’ayinsa ba. Amma da wuya su kan fito su faɗa saboda abin sai ya yi bambarakwai. Na amshi ƙorafe-ƙorafe da dama, amma yawanci sulhu ake yi.

Wacce ƙara ce ki ka tava shigarwa ko karewa da ta tsaya miki a rai har yanzu ba ki manta da ita ba?
Ƙarar wata mata ce da na shigar da ta nemi saki a wajen mijinta, inda ya yarda zai yi sakin amma da sharaɗin zai karvi yara ko kuma ya bar mata su, amma ba zai ciyar da su ba. Wannan mata ta yarda da wannan sharaɗi na yarda da riqe yaran tare da kulawa, kuma yaran sun kai har guda 8. Wannan abu ya tsaya min a rai sosai. Na yi mamakin jajircewar ta, shi kuma rashin kula da haƙƙin da ke kanshi ya bani mamaki matuƙa.

Idan da za a ba ki zaɓi ki canza aikin da ki ke yi, wanne aiki ki ke sha’awar yi ban da aikin lauya?
Gaskiya fannin aikin jarida zan zaɓa, don ina son aikin matuƙa. A taƙaice ma lokacin neman shiga jami’a ma shi na zaɓa da farko.

Kina da sha’awar shiga siyasa yanzu ko nan gaba?
Gaskiya dai Ina kallon siyasa a matsayin wani abu na rayuwa, don idan ka ce ba za ka yi siyasa ba to, tamkar ka sayar da ‘yancin ka ne na mai ka ke so ka zama, ‘yancin shiga makaranta da sauransu. Kamar kana bai wa mutane dama ne don zaɓar ma ka yaya za ka gabatar da rayuwarka ɗungurugum. Amma ba na sha’awar yin siyasa gaskiya a halin yanzu.

Yaya batun iyali, akwai yara ne?
E, ina da aure. Maigidana shi ma lauya ne ɗan’uwa na. Ina kuma da yara 6, mace ɗaya, maza biyar.

Barista Mariya

Yaya ki ke haɗa aikin ki na lauya da tafiyar da hidimar iyali?
Alhamdulillah, da taimakon Allah, bayan aikin lauya ma Ina aikin karantarwa. Dukka komai na tafiya bisa tsari ne, shi ya sa abin sai godiya, duk da dai gaskiya akwai ƙalubale, amma Allah na taimakona.

Wacce gudunmawa ki ke bayarwa a ƙungiyoyin al’umma na wayar da kai?
Na kan bai wa mata shawara su tashi su dogara da kansu wajen yin sana’a ko da a cikin gida ne, ko kuma aiki daidai ilminsu. Domin hakan na ɗebe kewa kuma yana rage raɗaɗin damuwa. Sannan hakan ma na rage yawan saɓani, domin yana hana yawan bani bani da ke kawo matsala saboda yanayi na yau da kullum. Tunda babu mai iyar wa ɗan Adam sai Allah.

Wanne abu ne ki ke yi na nishaɗi a lokacin da ba kya aiki?
Idan ba na aiki na kan kwanta ne Ina sauraron wa’azozi daga malamai a waya ko a talabijin.

Wacce shawara ki ke so ki bai wa abokan aikinki lauyoyi?
Shawara ta gare su ita ce, su tsaya tsayin daka wajen bin bayan gaskiya don ganin an yi adalci. Su kuma ɗauki aikinsu da muhimmanci, kar su wofintar da kansu. Su yarda da kansu a cikin al’amuransu dukka. Su guji bin bayan ƙariya ko da kuwa za su samu kuɗi ko ɗaukaka, domin ramin ta ƙurarre ne, ɗaukaka ta hakan ba mai ɗorewa ba ce.

Gaya mana wata karin magana da take tasiri a rayuwarki?
“Zuciya ɗaya Laya” ita ce karin maganar da ke tasirantuwa a rayuwata.

Mun gode.
Ni ma na gode da wannan dama da aka ba ni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *