Mazauna Abuja ku gabatar da sallar Idi a masallatan Juma’ar yankunanku – Hukuma

Daga AISHA ASAS

Hukumar Birnin Tarayya, Abuja, ta ce a masallatan Juma’a ne mazauna birnin za su gabatar da sallar Idi ƙarama.

Hukumar ta cim ma wannan matsaya ne yayin wani taro da Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello tare da tawagar majalisar malaman Abuja ƙarƙashin jagorancin Imam (Dr) Tajudeen M.B Adigun, suka gudanar Litinin a Abuja don tattauna yadda za a gabatar da sallar Idi mai zuwa.

Da yake jawabi, Ministan ya nuna godiyarsa ga malaman game da irin haɗin kan da suke bayarwa a fagen yaƙi da cutar korona a birnin tarayya.

Ministan ya ce bisa la’akari da ƙa’idojin da Gwamnatin Tarayya ta shata don ci gaba da yaƙi da annobar, hukumar Abuja ta fitar da nata sharuɗɗan da take buƙata mazauna birnin su kiyaye a lokacin sallar Idi mai zuwa.

Hukumar ta ce ba za a yi sallah a filin masallacin Idi da ke babbar hanyar Umaru Musa Yar’adua ba; ana buƙatar masallata su gabatar da sallar Idi a masallatan Juma’a da ke yankunansu; tarin mutane a masallatai kada ya haura kashi 50 cikin 100 na yawan mutanen da masallatan suka saba ɗauka.

Ana buƙatar hukumomin addinai su kula da shige da ficen mutane a wuraren ibada; a kula da batun rufe baki da hanci, bada tazara a tsakanin juna, tsaftace hannuwa, ba a yarda a buɗe wuraren shaƙatawa da makamantansu ba, da dai sauransu.

A nasa ɓangaren, shugaban tawagar malaman, Dr Tajudeen
Mohammed Bello Adigun, ya ce “A Musulunci, ana sauraron abin da masana da ƙwararru suka faɗa, kuma waɗanda suka tattauna da mu ƙwararru ne kan sha’anin kiwon lafiya. Sannan biyayya ga unarnin shugabanni abu ne da Musulunci ya yarda da shi.”

A ƙarshe, Dr Adigun ya yi kira al’ummar Musulmi mazauna Abuja da a kiyaye dokokin da aka shimfiɗa yayin sallar Idin da za a gabatar.