Mazauna da masu sana’ar POS a Kano sun koka kan Ƙarancin Kuɗi

Daga USMAN KAROFI

Mazauna Kano da masu gudanar sana’ar POS sun koka kan Ƙarancin Kuɗi da ke addabar jihar, wanda ke shafar kasuwanci da rayuwar jama’a.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa matsalar Ƙarancin Kuɗi na ƙara tsananta, inda ake fuskantar barazana ga kasuwanci da rayuwar al’umma a kullum.

Wani mazaunin Kano, Halliru Aƙilu, ya ce, “Wallahi, a yanzu akwai Ƙarancin Kuɗi sosai. Ni ban saba fita da kudi a hannu ba, abin da nake yi shi ne neman inda zan samu su idan na fita. Amma yanzu yana da wahala. Idan ka je wajen POS, sai ka samu ba su da kudi ko da naira dubu daya ko dubu biyu. Idan zan fita aiki, matsala ce saboda da wuya su amince da turawa ta waya sai da Kuɗi kawai.”

Ya yi kira ga hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa kan wannan matsala, yana mai cewa, “Ina kira ga hukumomi su duba wannan batu, domin muna shan wahala.

Shi ma wani mai POS mai suna A. A. Adamu ya bayyana yadda ‘yan kasuwa ke ƙin kai kuɗin su banki. Ya ce, “Tun watanni biyu da suka gabata muke fama da wannan matsala.

Ya ƙara da cewa, “Yanzu bankuna ba su da Kuɗi, misali idan ka buƙaci Naira N500,000, sai a ba ka N30,000 kawai. Wannan na shafar kasuwancinmu sosai. Daga gidajen mai da sauran kasuwanni ma haka suke ƙorafi.”

Ya kuma bada misali da cewa, “Akwai lokacin da na je gidan mai, suka ce suna tara kuɗin domin wani attajiri da ke buƙatar Naira miliyan N300. An ce wasu suna sayen kayan abinci a kasuwanni kai tsaye ba tare da kai kuɗin banki ba. Hakan ya sa ba Kuɗi a banki.