Mbappe ya zama kaftin ɗin tawagar Faransa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Watanni uku bayan shan kayenta a wasan ƙarshe na kofin Duniya, tawagar ƙwallon ƙafar Faransa ta buɗe wani sabon babi a duniyar ƙwallo, inda da dama daga cikin ‘yan wasanta suka yi ritaya, lamarin da ya bai wa Kylian Mbappe damar zama kyaftin ɗin tawagar don tunkarar wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Turai na EURO 2024.

Yayin wasan ƙarshen dai ƙarƙashin gasar kofin Duniya da ta gudana a Ƙatar anga yadda Argentina ta doke Faransa a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan tashi wasa 3 da 3.

Babban koma baya ga tawagar ta Faransa shi ne ritayar mai tsaron raga Hugo Lloris mafi dokawa ƙasar wasa kuma wanda ke rike da muƙamin kaftin, kuma wasu ke ganin Antoine Griezman ya fi dacewa da magajinsa, ko da ya ke miƙa muƙamin ga Mbappe baya rasa nasaba da rawar ganin matashin ɗan wasan a gasar kofin duniya.

Lura da ritayar mai tsaron raga Steve Mandanda da ke matsayin sauyi ga gurbin Lloris hakan na nuna dole Faransa ta yi amfani da Mike Maignan da ke taka leda da AC Milan a wasanta na gobe juma’a da za ta karɓi baƙuncin Netherlands a Stade de France.

Cikin watannin 3 dai, anga yadda aka kai ruwa rana game da tsawaita kwantiragin mai horarwa Didier Deschamps zuwa shekarar 2026 wanda ke jagorantar tawagar tun 2012 dai dai lokacin wasu ke ganin cewa Zinadine Zidane yafi cancanta da jagorantar tawagar, a bangare guda shi kansa Zidane ɗin ana ganin bukatar gurbin ce ta hana shi karvar aikin hotrarwa a mabanbantan ƙungiyoyin da suka yi masa tayi.

Olivier Giroud mai shekaru 36 mafi zurawa Faransa ƙwallo zai ci gaba da dokawa ƙasar ƙwallo Raphael Varane ya yi ritaya, hakazalika Karim Benzema wanda bai samu damar taka leda a gasar kofin duniya ba.