Daga AISHA ASAS
Tsayin shekaru ya zama wata al’ada a tsakanin masu nishaɗantarwa, musamman tsofaffin jarumai da suka samu shuhura a masana’antar finafinai ta Kudu, wato Nollywood na samun kansu a mawuyacin halin daga ƙarshe, har ya kai su ga neman taimako daga al’umma, ya Allah ko a sanadin ciwo, ko kuma talauci da ya yi masu katutu.
Kaso mai yawa na jarumai da suka amsa sunansu ta ɓangaren nishaɗantar da masu kallonsu, suka samu karɓuwa, daga ƙarshe sun yi kira ga al’umma da su kawo masu ɗauki, ko dai ta ɓangaren rashin lafiya da ke buƙatar kuɗin magani, ko ta neman kuɓuta daga talaucin da ya yi masu dabaibayi.
Waɗannan jarumai da ke sanya masu kallonsu nishaɗi ta hanyar qwarewar da suke da ita, ɗaya bayan ɗaya na faɗawa a mawuyacin hali na daga curuta da suka shafi mutuwar sashen jiki, ciwon suga, mutuwar wata gava da sauran curuta, sai dai abin takaici ba su tara abinda za su iya ɗaukar nauyin kansu ba har sai sun miƙo ƙoƙon baransu ga jama’a.
Shafin Nishaɗi na jaridar Blueprint Manhaja na wannan mako, zai kawo wa masu karatu wasu daga cikin shahararrun jaruman Nollywood da irin haka ta kasance a tare da su;
Amaechi Muonagor:
Shahararren jarumi Amaechi Muonagor, na ɗaya daga cikin jaruman da suka fito neman taimako ga jama’a kan matsalar rashin lafiya da yake fama da ita. Jarumin mai shekaru 61, ya bayyana cewa, yana fama da rashin lafiya da ta yi sanadin shanyewar ɓangare ɗaya na jikinshi, wanda ya shafi hannu da ƙafa. Sannan ya nemi taimakon al’umma da abinda zai iya siyen magungunan da yake sha.
John Okafor (Mr. Ibu):
A ‘yan makwanin nan shi ma sanannen jarumin barkwanci John Okafor, wanda aka fi sani da Mr. Ibu, ya biyo layi, duk da cewa tsakanin sa da na jarumi Muonagor ‘yan makonni ne. Shi ma dai ya nemi addu’ar mutanen Nijeriya da kuma taimako na kuɗaɗe kan tashi irin rashin lafiya. An yi wa jarumi Mista Ibu tiyata har bakwai, kafin daga baya aka yanke shawarar cire ƙafarsa ɗaya don ceto rayuwarsa.
Ifeanyi Ezeokeke:
Za ku iya tuna jarumi Ifeanyi Ezeokeke, da rawar da ya taka a ‘Ugo Shave Me’. Shi ma dai ya fito a kafafen sadarwa ya nemi a taimaka masa kan rashin lafiyar da yake fama da ita, wadda bai bayyana ba. Sai dai ya ɗauki tsayin shekaru yana fama da ciwon. Ba iya taimako ya nema kan ciwon ba, ya nemi a kawo masu ɗauki kan irin talaucin da yake tare da shi.
Duro Michael:
Shahararren jarumi Duro Michael, wanda duniyar nishaɗantarwa ta san shi da ƙwarewa wurin ƙawata zukatan masu kallo, ya faɗa hannun ciwon suga, wanda ya yi masa mugun kamu. Rashin lafiyar tasa ta soma ne a shekarar 2020, inda ta janye duk wani zarafi na jikinsa da na aljihu. Yanzu haka jarumi Duro Michael ya doga ne da ɗan abinda jama’a suke taimaka masa da shi don kula da kansa da kuma lafiyarsa.
Sule Suebebe:
Sanannen ɗan wasan Yarbanci Sule Suebebe na fama da rashin lafiya mai matuƙar ruɗarwa da ke shafar ƙafafuwansa, wanda har malamin Coci fasto Agbala Gabriel, da muƙarrabansa suka yi alƙawarin bayar da taimako ga jarumin na daga ilimin da suke da shi.
Iya Gbonkan:
Shahararriyar jaruma Margret Olayinka, wadda aka fi sani da Iya Gbonkan, ta taɓa zuciyar jama’a, bayan da ta fitar da faifan bidiyonta, tana kira ga masoyanta da su taimaka mata. A cikin bidiyon da aka sake a intanet, jarumar mai shekaru 64 ta bayyana cewa, duk da jimawa da ta yi tana bayar da gudunmuwa a masana’antar shirya finafina bata tara abinda za ta iya siyen mota ba. Ta nemi masoyanta da su taimaka mata da abinda za ta iya siya wa kanta mota, da kuma wanda za ta kammala ginin da ta fara a Osogbo, na Jihar Osun. Biyo bayan wannan bidiyon wani daga masoyanta kuma mamallakin Alexes Promotion,Omobolanle Olatise ya share wa jarumar kukanta, inda ya aika mata da mota ta hannun wani Mustapha Jayeola.
Abin tambaya a nan shi ne, shin mai ya sa da jarumi ya ɗan ja baya yake shiga halin matsayin rayuwa?
A wata tattaunawa da daraktan waƙoƙi mai suna Boloji Eso, ta kafar WhatsApp, ya sheda wa Blueprint cewa, kaso mai yawa daga jarumai da ke finafinai a faɗin ƙasar nan ana yi masu biya ne na zalunci. Ya kuma bayyana takaicin sa kan irin ƙarancin biyan da ake yi wa masu haska finafinan. Wanda ta ce, ko kaɗan ɗan abinda ake ba su bai kai da irin ƙoƙarin da suke yi ba.
“Ina so mu yi abinda ya kamata. Domin Ina fatan jarumai su dinga cin moriyar ‘ya’yan itatuwan da muka shuka a tare da su. lokuta da dama albashin nasu ko kaɗan bai kai yadda ma ake tsammanin sa ba. Don haka Ina so mu hau gaɓar da jarumai za su iya samun abinda ya kamata.
Idan aka duba a vangaren mawaƙa da kuma masu wasan barkwanci, za mu ga cewa tuni suka bar jarumai a baya,” inji shi.
Mista Boloji ya qara da cewa, “Ina so a ce ana daraja jarumai, ana biyansu yadda ya kamata, saboda gaskiya jarumai na Nollywood ba a biyan su yadda ya kamata. Bugu da ƙari kuwa ba mu da ilimin yadda za mu yi amfani da abinda muke samu, mu faɗaɗa shi don kare kanmu a lokacin da tauraruwarmu ta disashe. Duk da cewa, a yanayin yadda masana’antar finafinai ta Nollywood ke tafiya, idan ana zamani da jarumi ba lallai ba ne ya iya samun lokacin da zai gina kansa ta fuskar kasuwanci.
Misali, ba na jin ma ana ba wa jarumi lokaci ya je ya yi bitar rol ɗin da zai hau, ko ya yi gwajin abinda zai yi a fim.”
Za mu cigaba.