Me ya biyo bayan babban zaɓen Nijeriya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ai duk masu sharhi na magana kan abin da ya biyo bayan babban zaɓen Nijeriya na 2023 inda hakan ya kawo lokacin da shugaban da ke kan gado Muhammadu Buhari ke shirin ajiye mulki ranar 29 ga watan mayu don ƙarewar wa’adin mulkin saka gabaɗaya bisa tandain tsarin mulki. Bayan kammala zaɓen da aka haqqaqe ya fi kowanne raba kan ’yan Nijeriya ta fuskar bambancin addini da ƙabilanci har ma da vangaranci, hakan wani darasi da kowane mai hankali ya kamata ya zauna shi kaɗai ya yi nazarin makomar Nijeriya kafin ma a je ga makomar dimokraɗiyya.

Duk abun da mai mulki ko mai marawa mai muli zai yi sai da ƙasar hakan zai yiwu. Idan a na zaman doya da manja ba cigaba mai ma’ana da za a samu. Ko ma ba a ce komai ba sakamakon zaɓen ya sa magoya bayan ’yan takara in ka deve waɗanda su ka lashe zaɓen an tashi dutse hannun riga. Dama duk gasa ko zaɓe a kan samu wanda ya yi nasara da wanda bai samu nasara ba amma a wannan karon lamarin ya wuce haka saboda ba kawai shugabancin ne kaɗai a ke hankoron samu ba, a’a har ma da batu mai saurin haddasa fitina wato wariya kan addini.

Mu lura abubuwa uku sun zama manyan ƙalubale ga Nijeriya: nuna bambancin addini, ƙabilanci da yanki ko ɓangaranci. A sanadiyyar son zuciya don waɗanda muhimman abubuwan da ya dace su kawo zaman lafiya, wasu sun zuga jama’a a ka samu asarar rayuka da dukiya mai yawan gaske. Waɗannan abubuwa uku a baya kan zama a bayan fage musamman wajen zaɓen shugaban ƙasa, amma a wannan zaɓe abun a lasifika ake bayanin sa arara.

Kuma abun takaicin ma na kan gaba a dalilan wato addini in ka duba masu yayata lamarin ba sa la’akari da addini ko waɗanda su kan marawa bayan ba sa tada addinin su ko kishin addinin sai lokacin zaɓe ya yi. A nan a kan samu ’yan wannan addinin da kan dau matakin marawa ’yan addinin su baya don sun ga ’yan wancan addini na marawa na su baya. Idan mu ka lura da kyau za mu gane ba wani babban sauyi da a kan samu idan shugaba ya fito daga wani addini ta fuskar taimakawa addinin na sa.

Ba mamaki kawai in Musulmi ne a riƙa ganin sa in ya ga dama a masallacin jumma’a ko in Kirista ne ya riƙa zuwa majami’ar sa ranar Lahadi, shikenan. Waɗanda za su samu taimakon ba su wuce wasu ’yan ƙalilan daga jagororin addinan ba kuma su ɗin ma sai in sun cire kunya sun roƙa ko gaba daya sun sauka daga koyarwar addinin na su kafin shugaban ya kula su.

Shin ko dai burin zabar ɗan takara daga addinin mutum shi ne don dai kawai ka ji ya fito daga addini ka shikenan ko da ba ya tsoron Allah kuma ko da addinin bai dame shi ba. In mu ka koma kan ƙabilanci ma duk kanwar ja ce don in ka ɗebe yare da dan takarar ko wanda a ka marawa bayan zai yi lokacin kamfen, da zarar ya lashe sai sarki wani ko tsohon babban sakatare wane ne kaɗai za su iya ganin sa. In kuma ɓangaranci a ke magana irin jagororin nan da mu ke gani a Afurka sun fi son zama ’yan vangaren Landon, Jamus, Amurka da Dubai.

Maganar wai yankin na kaza maso kaza duk sai in zaɓe ya taso. Irin waɗannan mutanen su na da gidaje a ƙasashen turai da Amurka da Daular Larabawa ne, in haka ne me ribarmu ko ribarka? Ko ciwon kai su ka yi za ka ga sun garzaya wajen masu jajayen kunne ne don kula da su kai kuma ka na nan a asibitin garin ku da ba magani balle kwarerren likita. Ni fa na lura kawai rikicewa ta gangan ko son zuciya kan sa mutane marawa wani baya don jabilanci ko makamancin hakan. Ina amfanin inuwar giginya na nesa ke shan inuwar ta.

Gabaɗaya batun ‘MUSLIM-MUSLIM’ da wasu ke yi wato Musulmi da Muslmi su yi takara kan tikiti ɗaya ba abun da ya dace a duba ba ne har dai ’yan Nijeriya na ƙaunar junan su. To mene ne mabiyin wani addini zai rasa? A duba cancanta kawai shi ya fi alheri. Kuma idan wannan jam’iyya ta tsaida wanda bai kwanta ma ka a rai ba koma wata jam’iyyar ba tare da ƙarfafa wargaza kan jama’ar k aba cewa an nuna ma ka wariya.

Duk mutanen nan ’yan Nijeriya ne. Me zai hana wata jam’iyyar ta duba Kiristoci ko ’yan addinin gargajiya da su ka cancanta ta tsaida su takara ta kuma yi kamfen ba tare da duba addinin su ba? Ina mai tabbatarwa ’yan Nijeriya matukar za su daina kawo irin wannan tunani na bambancin addini da ƙabialnci to za a samu canjin da a ke buqata. Ba za mu rasa jin yadda a yanzu wasu Musulmi ke yabawa tsohon shugaba Jonathan ba wanda a lokacin da PDP ta yi baƙin jini a ka tsane shi har a ke cewa shi ya ke ɗaukar nauyin ’yan ta’adda don rage yawan ’yan arewa.

Shin da shugaba Buhari ya zo a masallaci ya tare ne? Hasalima shugaban ba ya fitowa babban masallacin ƙasa a Abuja don sallar Juma’a inda ya zabi yin sallar sa a Fadar Aso Rock. Dalilin da a ka bayar na hakan shi ne don kar zuwan sa ya sa a riqa takurawa jama’a. In an tuna zamanin marigayi Umaru Musa ’Yar’adua ya kan zo babban masallacin in ya fito a taru a na daga ma sa hannu, shikenan ribar talakawa kenan su ga shugaba da babbar farar riga ya na daga hannu sai kuma wani makon.

A gefe guda zamanin mulkin Goodluck Jonathan ya kan yi ibadarsa a babbar majami’ar Abuja inda tsohon shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya Ayo Oritsejafor kan shafa kan sa, shikenan, wace riba mabiyin addinin Kirista a Riyom ta jihar Filato ko Zangon Kataf a Kaduna ta kudu ke cin riba daga shafa kan Jonathan? Kawai yaudarar kai ne kan faru wanda ya dace mutane su farka daga bautar da kai su sani kowa zai iya rayuwa a Nijeriya kuma a samu duk nasara ko cigaban da a ke buƙata. Mu ma ƙara komawa kan mulkin shugaba Buhari, shin me ’yan Daura su ka amfana da shi fiye da abun da ’yan Legos su ka amfana da shi a mulkin?

Ba mamaki hutun da shugaban kan je Daura ya yi saukar angulu a da jirgi shikenan kawai tunanin ai dan garin mu ne. Haba ai wannan lokaci ya kamata ya wuce yayin da Nijeriya ta fara tsufa daga lokacin da a ka ba da ’yanci zuwa yanzu shekaru 63. Duk mai neman shugaban Nijeriya ya dace ya koma daga tushe tun yanzu da a ka kammala zaɓe nan ya fara neman jama’a da cusa ra’ayi mai ma’ana na yaƙi da talauci da babakeren ƙalilan daga ’yan boko da ba su da tuanin da ya wuce matan su da ’ya’yansu ba.

Duk manyan ’yan siyasa da manyan ’yan boko na da qabila daya da kan haɗa su a inuwa daya kuma wannan aqidar ita ce jari hujja. Kar ka ga kamar su na hamayya da juna ko kaxan ba haka ba ne su na qaunar juna kuma su na gamuwa su yi ta sheka dariya da zolayar juna. Shin ba mu ga lokacin kamfen Bola Tinubu ya yi kicivis da Atiku Abubakar a filin jirgin sama a Abuja ba su ka shiga sheka dariya da sabunta zumuntar da ke tsakanin su. Kuma matan su kan ziyarci juna su yi biki ko su tafi wani babban ɗakin taro su yi ta zunduma rawa don wani ɗansu ko ’yarsu ta gama makarnta a turai an haɗa ta aure da wani babban dan jari hujja.

Gagarumar tawagar ɗan takarar jam’iyyar PDP a babban zaɓen 2023 Atiku Abubakar ta yi zanga-zangar lumana zuwa hukumar zaɓe don nuna rashin amincewa da sakamakon.

Tawagar bisa jagorancin shugabannin PDP da Atiku Abubakar ta buƙaci a soke sakamakon.

Zanga-zangar da a ka daɗe ba a ga irin ta ba zuwa hukumar na zuwa ne bayan kotun ɗaukaka ƙara ta ba da hurumi ga ɗan takarar na PDP Atiku da na Leba Obi su duba kayan da a ka yi amfani da su wajen zaɓen musamman na’urar BVAS da ’yan adawarsu ka ce sam ba a yi amfani da ita ba.

Kakakin kamfen ɗin Dino Melaye ya ce sam ba za su amince da sakamakon ba kuma sun nuna hakan a lokacin da su ka fice daga ɗakin bayyana sakamakon gabanin kammala kawo sakamakon zaɓen.

Tawagar ta miƙa wasiƙa da ke ƙunshe da dukkan ƙorafe-ƙorafen ’yan adawar inda kwamishina mai kula da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a Festus Okoye ya karva ya yi alwashin mikawa shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu.

“Hukumar nan ba ta ɗaukar umurni daga wajen kowace jam’iyyar siyasa, aikin ta ga ’yan Nijeriya ne, za mu ɗauki mataki kan sashen wasiƙar da ya shafi shari’a kuma za mu duba dukkan abun da a ka rubuta,” inji Okoye.

In za a tuna bayan zaɓen 2011 gabanin zaɓen 2015, shugaba Buhari ya jagoranci irin wannan zanga-zanga zuwa hukumar zaɓen da samun rakiyar shugabannin APC ƙarƙashin John Odigie Oyegun.

Kammalawa;

Yanzu dai talakawa sun yi zaɓe kuma ko an yi adalci ko ba a yi ba ya kamata su fifita nunawa juna ƙauna don su ne ba ’yan jari hujja ba. Talakawa su kafa kawancen marar sa jari balle su samu hujja ta hanyar maida wuka kuɓe su ƙara duba abun da zai amfane su fiye da amfanin ’yan jari hujja da kan tashi fir a jirgin sama kamar tsuntsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *