Me ya haifar da bunƙasar cinikayyar Sin da Afrika duk da ɓarkewar annoba?

Daga AHMAD FAGAM

Duba da irin girma da tasirin yanayin mu’amalar cuɗanyar juna dake tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afrika, zamu iya cewa, alaƙarsu tana haifarwa ɓangarorin biyu kyakkyawan sakamako. Har kullum, ɓangarorin biyu na ci gaba da nuna aniyarsu da sha’awarsu na cigaba da yin mu’amala domin kyautata mokomar alummun dukka ɓangarorin biyu.

Duk da irin mummunan tasirin da annobar COVID-19 ta haifarwa duniya ta fuskoki da dama musamman wajen karya lagon tattalin arzikin ƙasashen duniya, amma alakar kasuwanci dake tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afrika tana samun tagomashi. Kamar yadda wani rahoton da kamfanin bincike da bada shawarwarin kasuwanci na Global research and advisory company dake birnin Oxford na ƙasar Birtaniya ya fitar kwanan nan, inda ya bayyana cewa, duk da irin ƙalubaloli da duniya ke fuskanta a tsarin hada-hadar kasuwanci, amma cinikayya tsakanin ƙasar Sin da kasashen Afrika ta samu gagarumar bunƙasuwa a shekarar 2021.

Koda yake, har kullum ƙasar tana yawan nanata ƙudurinta na tallafawa ƙasashe masu tasowa da kuma ƙulla dangantaka mai karfi tsakaninta da ƙasashen masu tasowar ciki har da ƙasashen Afrika, lamarin ya sanya ƙasar Sin ɗaukar wasu jerin matakai domin kyautata cuɗanyar kasuwanci tsakaninta da kasashen Afrika. Alal misali, a baya bayan nan, sakamakon sassauta dokokin kasuwanci da hukumar kwastom ta kasar Sin ta yiwa wasu ƙasashen Afrika, matakin ya bayar da damar samun ƙaruwar kayan amfanin gona daga nahiyar Afrika zuwa kasuwannin ƙasar Sin, kamar yadda rahoton jaridar turanci ta South China Morning Post, dake da babban ofishinta a Hong Kong ta wallafa.

A baya bayan nan, ƙasashen Afrika ta kudu, da Kenya da Zimbabwe, suna daga cikin ƙasashen da suka sanya hannu kan dokokin da aka yi wa gyaran fuska, lamarin da ya bada dama ga ƙasashen wajen samun shiga kasuwannin hada-hada na ƙasar Sin. A watan jiya, ƙasar Afrika ta kudu ta shigar da kashin farko na lemon tsaminta 100,000 zuwa ƙasar Sin.

Ƙasar Tanzania ma ta fara shigar da waken soyarta zuwa ƙasar Sin a shekarar 2020. Bugu da ƙari, an cimma makamanciyar wannan yarjejeniyar don shigar da avocados, da ganyen shayi, da kofi da furanni daga ƙasar Kenya zuwa kasuwannin Sin, sai kuma gahawa da waken soya daga ƙasashen Habasha da Rwanda, da naman shanu daga ƙasashen Namibia da Botswana, da kayan lambu daga ƙasar Afrika ta kudu.

Dukka waɗannan sun taimaka wajen ƙara ƙarfafa cudanyar kasuwanci tsakanin Sin da ƙasashen Afrika. Har kullum ɓangarorin biyu suna kara lalibo sabbin hanyoyin ƙarfafa hulɗarsu daga dukkan fannoni domin baiwa marada kunya.