Me ya kawo durƙushewar masana’antar fina-finai ta Kannywood?

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano

Tun bayan durƙushewar da Kasuwar Ƙofar Wambai da ke Kano ta yi kusan shekaru biyar da su ka gabata, masana’antar ta shiga cikin wani yanayin da babu wanda zai ce ga in da ta sa gaba.

Domin kuwa, ita ce kaɗai kasuwar da masana’antar ta dogara da ita wajen tafiyar da harkokin kasuwancin fina-finan da su ke yi, saboda duk in da fim zai je a faɗin duniyar nan in dai ta hanyar CD ne to dole sai ta kasuwar Ƙofar Wambai zai je in da a ke buƙatar ya je ɗin, saboda ita ce kasuwar fina-finan Hausa mafi girma tun bayan mutuwar kasuwar Bata.

Babban dalilan da su ka jawo mutuwar kasuwar Ƙofar Wambai dai guda biyu ne. Na farko, masu satar fasaha da su ka yi wa harkar kutse in da su ka yi ka-ka-gida wajen tafiyar da harkar kuma suka hana masu sana’ar cin moriyar sanar tasu. Domin a lokacin da furodusa ya saki fim ɗinsa a kasuwa, kafin a raba shi wasu jihohin su tuni masu satar fasaha sun baza shi har ma zuwa ƙasashen da muke maƙotaka da su, don haka a lokacin da furodusa yake shirin raba kayansa wasu jihohin, sai ya samu labarin tuni an gama kallon fim ɗin a can, don haka yana ji yana gani sai dai ya tura ɗan abin da ya sauwaƙa, wanda idan yana tura kwafi dubu uku sai dai ya tura duba ɗaya, daga ƙarshe ma wanda ya tura ɗin sai an dawo masa da kwantai.

Matsala ta biyu kuma, daina yayin CD da DVD da aka yi saboda cigaban fasahar zamani, wanda hakan ya sa aka daina saka fim a cikin DVD saboda harkar ta koma online, yayin da su kuma masu gudanar da harkokin sana’ar fim ba su shirya karɓar zamani ba, don haka sai kowa ya koma ba tare da neman ina ne mafita ba.

A maimakon haka ma sai wasu da suke da kuɗi a hannun su sai suka rinƙa zuba kuɗin suna ƙara yin fim suna kai wa kasuwa, wai a tunaninsu harkar za ta dawo bayan wani lokaci nan gaba, to sai ya zama abin suna yi kamar suna ƙara kuzawa agwagwa ruwa, domin kaɗan ne daga cikinsu suka waye da tunanin kai fina-finan su Gidajen Talbijin, da suka fara ɓullowa a ‘yan shekarun baya.

Kodayake, wayewar tasu ba ta jawo wa masana’antar komai ba sai ma ƙara durƙusar da ita da suka yi. Domin kuwa, sun yi amfani da wannan damar ne suka rinƙa karɓar fina-finan mutane da sunan za su kai musu, amma daga sun kai da yawa idan sun sayar an biya su kuɗin to ba za su dawowa da masu fim ɗin ba, sai kawai su yi harkar gabansu da kuɗin.

Wannan ya jawo da yawan furodusoshi da suka bayar da fina-finansu an hana su kuɗin sai dai kawai su ga ana haskawa a manyan gidajen talbijin, idan sun yi bincike sai su ji ai tuni an biya kuɗin tun kafin a fara haskawa, don haka sai harkar ta ƙara durƙushewa.

Samun rance ko tallafi daga Gwamnatin Tarayya wanda aka ware domin harkar nishaɗi da ‘yan masana’antar fina-finai ta Kannywood suka yi wanda wasun su sun samu miliyoyin kuɗi, an ɗauka zai kawo gyara take da farfaɗo da masana’antar. To sai dai hakan bai sa ta farfaɗo ba, domin kuwa mafi yawan su da suka samu kuɗin ba a harkar suka zuba shi ba, sai aka bi wata hanyar da shi.

Wasu suka yi ta sayen manyan motoci da kayan sakawa na alfarma tare da canza gidan da suke haya a ciki zuwa wanda ya fi shi. Wasu kuma suka zuba kuɗin a harkar noma harkar da ba su san ta ba kuma ba su san yadda ake yin ta ba, domin akwai wasu daga cikinsu da ba su taɓa zuwa ƙauye ba, ballantana su san yadda gona take da kuma yadda ake noma, amma suka je suka zuba kuɗi a cikin harkar, wadda a sakamakon da ya biyo baya, duk a cikinsu babu wanda ya girbi riba sai faɗuwa, nan masana’antar ta ƙara shiga cikin talauci.

Wasu kuma daga cikinsu da suka samu kuɗin sai suka bi zamani, sai dai ba su bi zamanin ba cikin wayewa da kuma yadda ake gudanar da harkokin kasuwanci a duniya. Don kuwa, da suka samu kuɗin sai suka ga yanzu an daina yayin fim a DVD sai fina-finai masu dogon zango, don haka sai suka zuba kuɗinsu suka yi, amma sai suka yi ba yadda a ke yin sa ba a duniya, don haka da yawan fina-finan da aka yi masu dogon zango ba su samu karɓuwa ba ko a gidajen talbijin da aka kai musu don su saya, ƙarshe sai asarar kuɗin suka yi.

A yanzu dai abubuwa sun tsaya cak! Harkar ta koma kai kuka ni tagumi, babu wani abu da yake gudana, sai mata ne suke sharafinsu, kullum sai ƙara shigowa suke yi suna baje kolinsu na neman manyan samari, don haka a yanzu idan ma akwai wani abu da ya rage a cikin harkar fim, to bai wuce karuwanci da kawalci ba. Allah ya kawo mana gyara.