Me ya sa Amurka da ta gaza wajen yaƙar COVID-19 ta riƙa aikata laifuffuka?

Daga CMG HAUSA

Jiya Alhamis ne, shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta yi sa-in-sa da ‘yan jarida, saboda tambayoyin da suka yi mata game da soke shirin tallafa wa al’umma kan yaƙi da cutar COVID-19 sun fusata ta, al’amarin da ya sake shaidawa duniya cewa, a matsayinta na babbar ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziki, muradun siyasa na gaban kome a Amurka, har da rayuwar al’umma, kana, ‘yan siyasar ƙasar da har kullum suke iƙirarin cewa, wai su ne masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama, sun yi biris da kuma keta hakkokin dan Adam a fannin rayuwa.

A halin yanzu, cutar mashako ta COVID-19 na ci gaba da yin muni a Amurka, amma har yanzu babu wata mafita da mahukuntan ƙasar suka dauka na kawo ƙarshen wannan matsala. Manazarta na ganin cewa, dalili kuwa shi ne, saboda yawan mace-macen ‘yan asalin Afirka da Spaniya gami da Indiyawan daji ‘yan asalin Amurka ya fi na fararen fata ‘yan ƙasar, ganin yadda ake yin biris da su a Amurka. Wannan abu ya sake shaida matsalar nuna wariyar launin fata da ta ki ci ta ki cinyewa a ƙasar.

A wajen taro na 49 na kwamitin kare haƙƙin dan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya dake gudana yanzu haka a birnin Geneva, wakilan ƙasa da kasa sun nuna matuƙar damuwa kan batutuwan da suka shafi keta haƙƙin yara, da daukar matakan da ba su dace ba da ‘yan sanda suke yi a Amurka.

A nasa ɓangaren kuma, zaunannen wakilin ƙasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, jakada Chen Xu ya nuna cewa, yadda jama’a ke jin daɗin rayuwa shi ne hakkin dan Adam mafi girma. A sabili da haka, ya dace ‘yan siyasar Amurka su kalli abubuwan da suka aikata da kyau.

Fassarawa: Murtala Zhang