Me ya sa jami’in kuɗin kamfanin sumuntin Ɗangote yin murabus?

Daga AMINA YUSUF ALI

A halin yanzu dai Babban jami’in kula da harkokin kuɗi a kamfanin sumuntin Ɗangote ya yi murabus daga muƙaminsa a kamfanin. 

A ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata ne dai Kamfanin sumuntin na Ɗangoten ya ba da rahoton barin aikin da babban jami’in kuɗin na kamfanin, Mista Guillaume Moyen, ya yi. 

Kamfanin ya bayar da sanarwar ne a yayin ganawa da hukumar canjin kuɗin ta Nijeriya. Inda ya bayyana cewa, Mista Moyen ya bar muƙaminsa ne, don ra’ayinsa na ƙashin kai kuma ya yi ne a ranar 30 ga watan Yunin 2022. 

Hakazalika, kamfanin ya bayyana cewa, a yanzu haka ma an naɗa Mista Gbenga Fapohunda a matsayin sabon babban jami’in kuɗi a kamfanin. 

“Wannan sanarwa ce ga hukumar canji ta Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki cewa, Mista Guillaume Moyen ya bar muqaminsa na babban jami’in kuɗin a kamfanin Sumuntin Ɗangote don dalilansa na ƙashin kansa”. Inji kamfanin. 

“Kuma kamfanin yana miƙa godiya ga Mista Guillaume Moyen a kan jajircewa da kuma gudunmowarsa ga kamfanin, sannann tana masa fatan alkhairi a kan rayuwarsa a nan gaba.  

Shi kuma sabon jami’in kuɗi na riƙon da aka naɗa a kamfanin, Mista Fapohunda, wanda ya gaji gadon Mista  Moyen, an bayyana cewa, ƙwararre ne ɓangaren harkokin kuɗi wanda yake da gogewa ta sama da shekaru 20. Wanda rahotanni sun bayyana har a ƙasashen waje ya yi aiki. 

Ya fara aiki ne a kamfanin Sumuntin Ɗangote a matsayin babban jami’in kuɗin na shiyya tun watan Maris ɗin shekara 2021 zuwa yanzu da aka naɗa shi babban jami’in kula da kuɗinka kamfanin gabaɗaya. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *