Me ya sa maza suke ƙaro aure? (1)

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanku da jimirin karatun jaridarmu mai farin jini ta Blueprint Manhaja. Allah ya sake haɗa mu kuma a wannan makon mai albarka. A wannan mako mun zo mu ku da warwara ta zare har da abawa a kan tambayar nan da take kawo ruɗani kuma take sanya rashin fahimta a tsakanin ma’aurata. Wannan ba komai ba ce illa maganar ƙarin aure. Za mu duba mas’ala daga ɓangaren mata da kuma maza. 

A ɓangaren macen aure a ce za a yi mata kishiya shi ne ma fi munin labari da ta taɓa tinkara a rayuwarta. Saboda hatta masoyanta suna shiga ƙunci. Har jajanta mata ake yi. Haka maƙiyanta har murna suke yi. Gani suke ma kamar ƙarshenta ya zo. An ɗauki abin a mummunar Abu Wanda wasu ke ganin an gama dake, bayan abun duka ba haka ba ne. Allah ne Ya ce a yi, amma mutane gabaɗaya an juya abin an daina masa kallon abinda Allah Ya ce,  an koma wata fuskar daban.

Haka ita matar a nata ɓangaren gani take ya ci amanarta ko wani laifi ta yi masa, ko ta kasa  ko ba ya sonta, ko ya daina yayinta da sauran abubuwa dai da ƙwaƙwalwarta da zuciya za su yi ta mata wasi-wasi. 

Ki sani ‘yaruwa, ba wai kasawa kika yi ko ba ya sonki ba, ko ya daina yayinki ba, kawai akwai dalilai da dama da suke sa maza su ƙara aure. Duk da wani lokacin ma dai suna ƙarawar domin kasawar ta gidan. Amma ma fi yawancin lokuta suna auren ne saboda waɗannan dalilai masu zuwa:

  1. Ƙaddara: Na farko ƙaddara, Hausawa dai sun ce ta riga fata. Duk yadda mutum ya so abu ko ya ƙi shi, matuƙar yana cikin ƙaddararsa ba makawa sai ya same shi. Kuma ƙaddara ita ce dukkan abinda Allah ya rubuta zai samu bawa. Wato kamar arzikinsa, aure mutuwa da makamantansu. Idan akwai auren mace fiye da guda ɗaya ko haihuwar wasu yaran jikin wata macen bayan ke, a zane a cikin littafin ƙaddarar mijinki dole sai ya yi. Idan kika ɗau hanyar hanawa za ki iya mutuwa ko ki bar gidan kuma a yi.

Haka ke ma idan an rubuta miki samun kishiya a ƙaddararki, ba wani abu da zai hana sai an yi. Don haka abu ma fi sauƙi ki rungumi ƙaddararki ki nemi taimakon Allah ya kawo miki mafita. Ki toshe kunnenki daga masu famfo kin fi ƙarfin kishiya kaza-kaza. Daga ƙarshe a bar ki da cizon yatsa. An yi wa matan da suka fi ki kyau, dukiya, sarauta da komai ma kishiya. Amma ba su ɗaga hankali ba. Ke wacece da za a ce kin fi ƙarfi?

  1. Ra’ayi: Hausawa dai sun ce, ra’ayi riga ne. Idan namiji yana da ra’ayin zama da mace fiye da ɗaya, duk kulawarki gare shi da kyautata masa ba zai hana shi kawo wata cikin gidansa ba. ‘Yaruwa ba wanda kika yi wa laifi, ra’ayinsa ne haka. Idan kika ta da hankali ma ke dai ce za ki wahala. Gara ki bi a sannu. 
  2. Al’ada: Akwai al’adar Bahaushe da ya yarda cewa gazawa ce take sa a zauna da mace guda. Duk iliminsa da wayewarsa in dai sun ɗebi shekaru da mace guda, kuma yana da halin ƙarin, sai ya ƙaro. Sai dai idan ba shi da ra’ayi ko ƙarin ba ya cikin ƙaddararsa. Mazan da suka taso a gidajen da suke da auren mata da yawa sun mai da abin farilla ma kuma abin alfahari. To ya ga Ubansa, ƙannen Ubansa, Yayye, wani ma har ƙanne maza sun yi ƙari, ai gani yake idan bai yi ba ya zama saniyar ware ko na baya a dangi. Haka masu sarautun gargajiya dole a al’adance sukan tara mata har da ƙwarƙwarori. Kin ga wannan ai ba rashin so ne ya jawo ba ko?
  3. Iyayen dangi: Wani namijin kuma yana ƙaro aure sakamakon matsin lamba daga iyaye ko dangi. Wani lokaci iyaye kan yi fushi da shi idan bai ƙaro aure ba. Wani lokacin ma har haɗa shi ake da wacce ake son ya aura ɗin. Ba ma shi ya ce yana so ba. Wannan kuma ba abinda zai same ki ya gaya miki ba ne. Don haka, kada ki ta da hankalinki. Wataƙila ma rabin son da yake miki ba ya mata. Idan kuma kika tayar masa da hankali, da ma ga matsin lamba yana fama daga danginsa, kinga za ki tinzura shi ki fice masa a rai har ma girmanki ya faɗi a idonsa. 
  4. Na biyar, rashin haihuwa: Maza suna ƙara aure domin su samu zuriyya. Ko dai matarsa ba ta haihuwa kwata-kwata, ko kuma mai sha’awar cika gida da yara ne. To irin wannan duk me za ki yi na kyautata masa dole sai ya ƙara. Wata gani take ya ci amanarta don ya ƙaro aure idan ba ta haihuwa. To amma ‘yaruwa idan kina sara ki dinga duba bakin gatarin. Son kai ne a ɓangarenki ki yi baƙinciki don ba kya haihuwa ya ƙaro aure. Kada ki ji haushin mijinki. An san da ciwo sosai. Amma fa ba zancen cin amana Allah ne ya ba shi damar ya ƙara. Ke ma kuma Allah bai manta ki ba, akwai abinda ya tanadar miki. 
  5. Rashin gamsuwa: Akwai hikima da ta sa Allah ya ce namiji ya auri mace fiye da guda ɗaya. Wani namijin ba ya samun gamsuwa da mace guda. Wani ma yana tausaya miki kada ya fiye takura miki ki cutu. Ko kuma shi cutu ɗin. Don haka, sai ya ƙara aure biyu, uku zuwa har huɗu ma dai-dai da buƙatarsa. Don ya kare mutuncinsa.
  6. Gasa: Wasu mazan suna da gasa a kan komai, har ma da ƙaro aure. Kamar yadda na faɗa a baya, namijin idan ya ga ‘yanuwansa ko abokai sun yi aure, shi ma Allah-Allah yake shi ma ya ƙara. Abin ya zama gasa kenan. Wani ba shi ƙarfin yin amma saboda kada ya zama saniyar ware a abokai, sai ya taro aradun kawai da faɗin kansa. Wani ma karo-karo za a masa don shi ma ya shigo layin. Wannan kin ga naki ido ne. Waɗanda suka yi masa karo-karo ya yi aure ba za su cigaba da yi masa jigilar ɗawainiyar iyalinsa da suka ƙara yawa ba. 
  7. Ƙaruwar arziki: Hausawa sun ɗauka idan arzikinka ya ƙaru yadda za ka canza sabon gida wanda ya fi na sa, ka canza mota ka ƙara ɗaukaka rayuwarka haka za ka ƙaro mata. Har ma abin ya zama jiki ya zama doka. Mutane ma sun ɗauka hakan ya zama dole ma. Har ma idan kuɗinka ya ƙaru ba ka ƙara wata matar ba ake maka zargin anya lafiya kuwa? To don haka ta faru za ki ga an ci amanarki kuna tare tun ba komai amma yanzu kuma dare ɗaya Duniya ta samu, an ƙaro miki kishiya.

To ‘yaruwa gode wa Allah ya kamata ki yi a nan. Da Ya sa mijinki mai hangen nesa ne bai tattago miki wannan rigimar tun kuna cikin halin talauci ba. Kuma ki sani, arzikinsa shi ya nemi kayansa Allah ya ba shi ba zancen gori tunda ba ke kika ba shi ba. Haƙuri da kika yi da babu da talaucinsa a baya duk ladanki na wajen Allah. Idan kika yi gori kuma, tsaf ladanki za ki zobe. Babban abinda zai zama matsala idan ya ƙi amfana miki dukiyarsa sai wata wacce ya auro. Shi ma wannan ki yi haƙuri ki kai wa Allah ƙararsa na tabbata ma ji roƙo ne. Kuma ko ba ki kai ƙara ba, Allah yana gani. Sannan kuma kar ki manta duk abinda Allah ya nufa bawa zai samu rabonsa ba ya wuce shi. Don haka, bi a sannu. 

  1. Tausayi/taimako: Wani namijin yakan yi aure ma ba tare da ya shirya yi ba sai don tausayawa. Wasu mazan kan auri matan ‘yanuwansu da abokai da suka riga mu gidan gaskiya. Wasu ma haka kawai sukan ji tausayin bazawara uwar marayu, su aura don kula da yaranta. 

Haka sukan auri bazawara ko budurwa wacce ta samu jinkirin aure. Waɗannan nau’in aure duk jihadi ne da taimako. Ki ɗauki kanki ko ‘yarki ko ‘yaruwarki a matsayin waɗancan ‘yammata ko zawarawa, ai kinga taimako ne ko? To ke ma idan hakan ta faru da ke, mijinki ba sonki ne ba ya yi ba taimako ne. Ki goya masa baya. An san da kishi. Amma ba ki san inda rana za ta fa]i ke ma a kanki ko zuriyyarki ba. Ranar da Allah ya ga dama zai iya juya al’amarinsa kuma ke ma za ki so ki samu irin wancan taimakon. 

  1. Auren jari: Wasu mazan fa ba don komai za su auri mace ba sai don abin hannunta. Ke ta gida kina can kina iskar kishi. Wani sam ba soyayya ce tsakaninsa da matar da ya ƙaro miki ba, kawai shi so yake ya raɓe ta ya nasu da maiƙon da take da shi. Sai ki bi a hankali don irin waɗannan matan wuf, sukan ƙwace miji kamar walƙiya. Sai a nutsu.

A nan muka kawo ƙarshen jawabinmu na wannan mako. Saboda tsawon wannnan mas’ala ba zai yiwu mu kammala ba dukka a wannan makon. Za mu cigaba a mako mai zuwa insha’Allah. A mako mai zuwa za mu taɓo ɓangaren maza a kan zancen ƙarin aure.

Masu kirana a waya su yi min addu’a su ban shawarwari da tsokaci ina godiya. Kuma kuna ƙarfafa ta. Kuma kullum ƙofar tattaunawa a buɗe take tsakaninmu.