Me ya sa MDD ta ayyana tashar sararin samaniyar ƙasar Sin tamkar babban abin koyi

Daga CMG HAUSA

Yau Asabar da safe misalin da ƙarfe 10, ɓangaren dawowa na kumbon Shenzhou-13 na ƙasar Sin ya sauka doron duniya lami lafiya. ‘Yan sama jannati 3 da ke cikin kumbon sun kammala aikinsu a sararin samaniya har na tsawon watanni 6, inda suka dawo gida.

Yayin da ake murnar samun nasarar dawowar ‘yan sama jannatin 3 na ƙasar Sin duniyarmu, abin da ya kamata a tuna da shi, shi ne da wuya ƙasar Sin ta samu irin wannan nasara. Bayan da ƙasar Sin ta tsara manyan tsare-tsare na matakai 3 na ganin ‘yan sama jannati sun yi tafiya cikin kumbo a sararin samaniya a shekarar 1992, ƙasar Sin tana nacewa kan tsayawa da ƙafafunta a fannin yin ƙirƙire-ƙirƙire, ta kuma inganta hadin gwiwa da ƙasashen Rasha, Japan da Turai, a ƙoƙarin samun ci gaba a mataki-mataki.

Yau an samu cikakkiyar nasarar gudanar da aikin kumbon Shenzhou-13. Ƙasar Sin ta shiga matakin ginin babbar tashar sararin samaniya. Wataƙila nan da shekaru da dama masu zuwa, tashar za ta kasance tashar sararin samaniya daya tak a sararin samaniya, lamarin da zai zama babbar nasarar al’ummar ƙasar Sin ta fannonin kimiyya da fasaha, kana kuma zai zama mafarin sabon matakin nazarin sararin samaniya ga dukkan ‘yan Adam.

Har ila yau tashar sararin samaniyar ƙasar Sin za ta bude ƙofarta ga dukkan ƙasashe mambobin MDD a karo na farko a tarihi. Yanzu an tanadi ayyuka guda 9 daga ƙasashe 17 da rukunoni guda 23 cikin jerin ayyuka a rukuni na farko, wadanda za a gudanar da su cikin tashar sararin samaniyar ƙasar Sin.

Dangane da lamarin, madam Simonetta Di Pippo, darektar ofishin kula da harkokin sararin samaniya na MDD ta bayyana cewa, tashar sararin samaniyar ƙasar Sin da za ta bude kofa ga kowa, wani muhimmin ɓangare ne na shawarar MDD ta yin amfani da sararin samaniya tsakanin ƙasa da ƙasa, ta kasance wani babban abin koyi.

Mai Fassara: Tasallah Yuan