Messi ya ci wa tawagar Argentina ƙwallo ta 100

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A daren Talata ne kaftin ɗin Argentina, Lionel Messi ya ci ƙwallonsa ta 100 a wasannin da ya buga na ƙasa da ƙasa, a karawar da ƙasarsa, Argentina ta lallasa Curacao da ci 7 da nema.

Messi, wanda sau 7 ya ke lashe kyautar gwani na gwanaye a harkar ƙwallon ƙafar duniya, wadda ake kira Ballon d’Or, shi ya fara saka qwallo a raga a cikin minti na 20 da fara wasan da aka kara a birnin Santiago del Estero.

Wannan na zuwa ne shekaru 17 bayan da ya fara ci wa Argentina ƙwallo a wasan da ta sha kashi a hannun Croatia 3-2 a watan Maris na shekarar 2006.

Ɗan wasan mai shekaru 35 dai ya ci ƙwallaye 3 ne rigis a wasan na daren Talata, abin da ke nuni da cewa karo na 7 kenan ya yi haka a tawagar ƙwallon ƙafar ƙasarsa.

Messi ya fara wasan na Talata ne ba kawai a matsayinsa na wanda fi kowa cin ƙwallaye a tawagar Argentina ba, sai dai baya ga hakan, ya shigo a matsayin wanda ya zarce shahararun ’yan wasa irin su Gabriel Batistuta mai ƙwallaye 56 da Sergio Aguero mai ƙwallaye 41.

Yanzu ƙwallayensa na ƙasa da ƙasa 102, a yayin da abokin hamayyarsa, Cristiano Ronaldo na Portugal ke da 122, sai Ali Dei na Iran mai 109.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *