Messi ya yi hawaye saboda alhinin ficewa daga Barcelona

Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafar nan, Lionel Messi, ya yi hawayi a baina jama’a saboda alhinin barin ƙungiyar ƙwallon ƙafar da ya shafe shekaru yana buga mata wasa, wato Barcelona.

Messi ya zubar da hawaye ne a lokacin da yake ƙoƙarin yi wa taron manema labarai bayani dangane da ficewarsa daga kulob ɗin Barcelona a Camp Nou.

A ranar Alhamis da ta gabata Barcelona ta tabbatar wa duniya cewa zakaran ƙwallon ƙafar, ɗan shekara 34 da haihuwa, ba zai sabunta kwantiraginsa da ƙungiyar ba saboda matsalar kuɗi da kuma shirin sake wa ƙungiyar fasali.

Messi ya shaida wa manema labarai ran Lahadi cewa, “A ‘yan kwanakin nan, na yi ta tunanin abin da zan faɗa wa duniya.

“Gaskiyar ita ce, na kasa tunanin komai. Wannan al’amari ne mai wahalar gaske a gare ni bayan shekaru masu yawa, rayuwata baki ɗaya a nan nake. Gaskiya ban shirya ma hakan ba.”

“A wannan shekarar, ni da iyalina mun gamsu kan cewa ba za mu ko’ina ba za mu zauna a gida, wannan shi ne abin da muka so.

Messi na hawaye

“Mun yi zaton za mu ci gaba da zamanmu a Barcelona. Mun ji daɗin zaman da muka yi a nan sosai. Ga shi yau, tilas in yi bankwana da komai.”

Sahihan bayanai sun nuna cewa, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint-Germain ta kusa cim ma yarjejeniya tsakaninta da Messi duk da alamu sun nuna akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakanin tauraron da kulob ɗin Manchester City sama da watanni 12.