Miƙa mulki: Ko kwana guda Buhari ba zai ƙara ba bayan cikar wa’adin mulkinsa – Boss Mustapha

Daga BASHIR ISAH

Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa don tabbatar da Shugaba Muhammadu Buhari ya miƙa mulki ga Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, ya zuwa 29 Mayu.

Mustapha ya ce ko kwana guda Buhari ba zai ƙara ba bayan cikar wa’adin mulkinsa ran 29 ga Mayu mai zuwa.

Ya bayyana haka ne a wajen taron Kwamitin Miƙa Mulki da ya gudana ranar Talata a Abuja.

Mustapha ya ce duk da ƙararrakin da suka taso dangane da zaɓen Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ba zai ƙara kwana ɗaya a matsayin Shugaban Ƙasa ba bayan ƙarewar wa’adinsa.

A cewarsa, “Shugaba Muhammadu Buhari ba zai ƙara ko kwana ɗaya ba bayan cikar wa’adin mulkinsa a ran 29 ga Mayu inda zai miƙa mulki ga wanda INEC ta ayyana.

“Tsare-tsaren kotu za su ci gaba, kuma muna bakin ƙoƙarinmu wajen tabbatar da tsarin miƙa mulki bai gamu da cikas ba,” in ji Mustapha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *