‘Mijina ke ƙarfafa ni kan aikina duk lokacin da gwiwata ta yi sanyi – Halima Hassan Ibrahim

“A dalilin aikin jarida na zama mai tallafa wa marayu”

Daga ABUBAKAR M. TAHIR

Masu karatu, wannan tattaunawa ce ta musamman da Wakilin Manhaja, Abubakar M. Tahir, ya yi da wata matashiyar ‘yar jarida kuma mai fafutukar tallafa wa marasa gata da gajiyayyu, wato Halima Hassan Ibrahim. A cikin tattaunawar da matashiyar ’yar jaridar mai shekaru 33, za ku ji yadda ta fara wannan aikin na tallafawa marayu da gajiyayyu, gwagwamayar rayuwa, nasarori da dai sauran batutuwa:

Mu fara da tarihinki a taƙaice.
Assalamu alaikum warahamatullah, ni dai Halima Hassan Ibrahim Shi ne sunana, kuma an haifeni a Kano, a Shekarar 1988, kenan ina da shekaru 33 zuwa yanzu. Nayi makarantar firamare dake ‘A tarauni special primary’, daga nan na tafi GDSS Giginyu inda nayi sakandare a nan.

Tunda farko, Ina da burin zama ma’aikaciyar asibiti, hakan yasa na nemi ‘School of Nursing’ har sau biyu ban dace ba, daga nan na tafi Jami’ar Bayero da zumar karanta inda na karanci ‘Industrial Chemistry’, sai dai hakan ba ta samu ba, kasancewar kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwa, Allah bai sa ina cikin waɗanda za su ci abinci ta wannan ɓangaren ba, sai na karanci aikin jarida wato ‘Mass Communication’ inda na kammala a 2012.

Bayan kammala karatuna lokacin mulkin Gwamnan Kano Engineer Rabi’u Musa Kwankwaso, ina ɗaya daga cikin waɗanda ya bamu aiki inda na fara da gidan talabijin na Abubakar Rimi wato ARTV, nayi aiki dasu har na tsawon shekara biyu.

Bayan na yi aure, na dawo Jigawa da zama, na samu aikin koyarwa a wata makarantar kuɗi wato ‘May Excellence International College’ inda nake koyar da turanci.

Ina koyarwa haka kuma ina aiki da wata ƙungiyar sa-kai ta Mafita, inda muke koyawa mata sana’o’in hannun, kamar ɗinki, saƙa, kitso da dai sauran sana’o’i na dogaro da kai ga ‘yan’uwa mata.

Da ya ke ina bibiyar jaridu, kwatsam wata rana ina karanta jaridar ‘Daily Trust’ sai na ci karo da tallar neman ma’aikata da Sawaba Fm take, wannan yasa na cika, inda kuma suka gayyace mu tantancewa a ɗakin karatu na Jihar Kano wato ‘State library’.

Kusan watannin bakwai da yin tantancewar na ma manta da na cike aiki dasu, sai ga takarda daga gidan rediyon suna tayani murna inda aka ɗauke ni aikin mai gabatar da ‘program On air Personal'(OAP) wato wanda ake jin muryansu, kuma har zuwa yanzu da muke tattaunawa da kai ina kan wannan matsayin. Alhamdu lillah muna ƙoƙari, kuma mutane suna nuna gamsuwarsu kan ƙoƙarin da muke yi.

Mene ne ya ja ra’ayinki ki ka fara aikin jin ƙai?
Eh to, a gaskiya hakan ya faru ne sakamakon ambaliyar ruwa ta tashin hankali da akayi a Hadejia wanda ta fara daga ranar Asabar, gaskiya munga tashin hankali a wannan lokaci.
To a matsayina na ‘yar jarida, munje ziyarar aiki, domin ganin yadda ake ƙoƙarin ceto garuruwan dake cikin wannan iftila’in na ambaliya da kuma duba irin taimakon da ake buƙata a yankunan. To a gaskiya mutane suna cikin wani hali, wasu suna kwana kan titina, mata wasu na kwana a gidajen mai.

Bayan dawowa ta gidan Radiyo, akwai lokacin da ake bamu na tattauna muhimman batutuwa, Hakan yasa na ke sanar da mutane cewa ana buƙatar tallafin gaggawa domin kare waɗannan ƙauyuka daga wannan iftila’i.

Wannan yasa Mata da Maza, mutanen birni da ƙauye suka rinƙa kawo kayan agaji, a lokacin mun samu kuɗi mai tarin yawa, har ma da kayan abinci, domin yin wannan aikin.

Muka siye katifu na ƙasa masu yawa domin agazawa waɗannan bayin Allan. Da kuma wasu ababe na buƙata da muka haɗa masu da su.

To shi ne fa, bayan fita daga cikin wannan jarabawar sai ya zama al’umma suna kallona a matsayin wata jaruma wanda tayi abin azo a gani, har ana jinjina mini, mutane suna kira na suna min sam barka. To sai al’umma suke zuwa takanas guna domin neman tallafin kayan abinci, rashin lafiya, kuɗin makaranta da sauransu.

Na kan ɗauka a aljihuna na siya musu, in kuma abin babba ne nakan ɗora a shafina na ‘Facebook’ inda masoya sukan tallafa har akai ga biya wa mutum wannan babbar buƙatar.

Shin kin buɗe gidauniya ne ko kuwa kin tsaya a iya ɗorawa a shafiinki na sada zumunta?
A gaskiya mutane da yawa sun bani shawarar buɗe gidauniya bayan cigaban da muka samu, kuma na karɓi shawarar su har ma na saka mata suna ‘Home For Orphans and needy Foudation’ (HONAF).

Kafin nan nakan bibiyi mata irina, masu ƙoƙarin tallafawa, to ta nan ne na fahimci ina buqatar ɗaukar wani ɓangare daga cikin ɓangarori na tallafawa. Hakan yasa na zaɓi ɓangaren tallafawa marayu da kuma marasa lafiya.

Na fara da kai wasu marayu makaranta, kuma gaskiya malaman makarantar sunyi murna da wannan ƙoƙari nawa, hakan ne ma yasa suka ƙi karɓan kuɗaɗen ɗaukar yaran.

Nice na zame musu uwa da uba, komai na kan musu, kuma alhmdu lillah yaran suna karatu yadda ya kamata, kusan sune akan shafinmu na yanar gizo na (HONAP).

Haka ta ɓangaren rashin lafiya, nakan kai mutum asibiti a bashi magani har ya samu lafiya. Misali akwai wani maras lafiyar ƙwaƙwalwa yana tafiya a titi yana bara, na kai shi asibiti, na siya masa magani, na kuma gyara masa gidansa, alhamdu lillah ya samu lafiya. Akwai lokacin da wani maras lafiya ɗan Kaugama yana fama da cutar lakka to gaskiya bani da kuɗin yi masa aiki hakan tasa na fitar da sanarwar neman tallafi a shafin sada zumunta, kuma mutane sun tallafa har aka yi nasarar samun lafiyarsa.

Kin sanar da mu cewa, akwai tallafi da gidauniyar ke bada wa a jikin kanta, sai idan matsalar tafi ƙarfin aljihunta ake neman taimakon wasu. Shin ta ina gidauniyar take samun kuɗaɗen gudanar da ayyukan da ku ke yi?
To alhamdu lillah da yake aikin tallafawa al’ummar annabi ne, jama’a ne ke bada gudunmawa, da kuma ɗan abin da yake a na wa aljihun. Bani mantawa, na yi shirin tallafawa al’umma a wani azumi da ya gabata, hakan tasa muka fitar da sanarwa a shafinmu na HONAP. Alhamdu lillah sun samu tallafi buhun shinkafa guda biyar da gero biyar haka kuma Akwai Ɗan Ɗakan Hadeja marigayi, da yake yana bibiyar aikinmu, hakan tasa ya bamu maqudan kuɗaɗe don yin wannan aiki na jinƙai, haka zalika muna samun tallafi daga al’umma daban-daban.

Kuma mu nyi nasarar bada tallafi na musamman, domin a kullum mukan bama marayu 40 abinci tsawon watan Ramadan, kasancewar mun samu tallafi mai yawa, bayan ciyarwa na dafafen abinci, mun raba ɗanye ga marasa ƙarfi, kamar zawarawa, Makafi, da dai sauran marasa ƙarfi bayin Allah. Aƙalla mutane 100 sun sami wannan tallafin.

Haka kuma a wannan shekarar mun samu tallafin kayan sawa masu yawa, waɗanda suka ba wa marayun mu damar yin adon salla kamar ko wane ɗa da ke da uba.
 
Waɗanne nasarori ne ki ka samu a wannan gidauniyar dama rayuwarki bakiɗaya?
Gaskiya mun gode Allah, mun samu ɗimbin nasarori. A ƙashin kaina ina da burin ganin na shiga sahun masu tallafawa al’umma da abinda suke dashi, cikin hikimar Allah gashi muna kan hanyar. Ina jin daɗin ganin wani na farin ciki ta sanadiyyata.

Na biyu a HONAP, mun sami tallafin Filoti biyu da rabi daga wani ɗan kasuwa inda muke fatan fara ginin makaranta da ma gidan marayu nan ba da daɗewa ba, da yardar Allah. Banda kuma dubun godiya da sa albarka da nake samu daga mutane manya da yara.

Ta ya ki ke iya tauna taura biyu a lokaci ɗaya, wato aikinki na jarida da kuma gudanar da ayyukan gidauniya, a gefe ɗaya ga hidima da iyali?
To, gaskiya abu ne mai wahalar gaske, ganin yadda muke fama da aiki a matsayina na (OAP) ga kuma shiga lungu da saƙo wajen tallafawa marasa ƙarfi. Duk da cewa mijina na ƙarfafani duk sanda na gaji, yakan cemin, raggo baya suna, kuma hidimtawa al’umma jihadi ne babba mai tarin lada.

Waɗanne ƙalubale ki ke fuskanta a wannan tafiya?
Ƙalubalen bai wuce yadda mutane suke kallon ba za mu iya ba, da kuma rashin samun sukuni, a ko wane lokaci mune asibiti, ƙauye, makaranta, akwai gajiya a matsayin mu na ‘yan Adam.
 
Wane kira ki ke da shi ga mata matasa irinki kan shigowa irin wannan gwagwarmayar?
To gaskiya ina kira ga mata matasa irina su zo su shigo irin wannan aiki. Mu sani mune zamu taka muhimmiyar rawa kan taimakawa kanmu wajen samo wa kanmu ‘yanci. Mu shiga ko wane aiki ayi da mu, ya zama ana damawa damu domin samar da al’umma ta gari mai ilimi da sanin ya kamata.

Wane kira ki ke da shi ga gwamnati, masu hannu da shuni da ma sauran al’umma?
Gaskiya kiranmu ga gwamnati shi ne; su rinƙa kula da waɗannan gidauniyoyi na taimakawa marasa ƙarfi, mune muke kusa da al’umma, mu muka san adadin mabuƙata. Idan sun tashi bada tallafi, su rinƙa duba irin waɗannan ƙungiyoyi don samun isar taimakon ga mai buƙatarsa.

Haka kuma muna kira ga masu hannu da shuni su rinƙa tallafa wa waɗannan ƙungiyoyi domin gina lahilarsu, saboda tallafa wa marayu sadaƙa ce mai ɗorewa, ko ba komai ka rinƙa tuna cewa kaima wata rana za ka iya zama marigayi ‘ya’yanka zasu iya fuskantar wannan matsala.

A ƙarshe muna kira ga al’umma da su ci gaba da bamu haɗin kai domin samun damar gina wani mutum wanda zuwa gaba zai iya bada gudummawa wajen ci gaban ƙasa bakiɗaya. Mu sani ilimi shi ne makamin da ake amfani da shi wajen yaƙar ayyukan ta’ addanci.

Haka kuma ina kira ga mata da su shigo aikin jarida ganin yadda ake fama da ƙarancin mata a wannan ɓangaren. Su sani shima aiki ne mai muhimmanci ga rayuwar al’umma duk da haɗarorin dake cikinsa, amma ya zama dole ace mun shige shi.

Haka kuma ina godewa dukkan waɗanda ke irin wannan aiki na jin qai. Kuma ina mai ba su ƙwarin gwiwa da cewa, kada su manta ladan wannan aikin tana wurin Allah ba mutum ba.

Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.