Mijina ne babban abokina – Halima Ahmad Dahir

“Rashin jajircewa ne ke hana mata ‘yan jarida kai wa sama”

“Mata da yawa ba sa kai tunaninsu kan yadda za su taimaki mazansu a sana’arsu”

Daga AISHA ASAS

A yau dai shafin Gimbiya ya ɗauko wa masu karatu wadda ta cancanci mata su kirata da Gimbiya, kasancewar ta jajirtacciyar mace kuma abin koyi ga mata. Mai karatu zai amince da hakan ne ta irin nasarorin da ta samu a ɓangarorin da mata da yawa suke ganin mata ba sa samun kai. Jajirtacciyar ‘yar jarida ce da ta kai matsayin riqe babban matsayi a aikin jarida, kuma ta kwashe tsayin shekaru ashirin da takwas a cikin sa. Baya ga haka, ta zama abin koyi ga mata ta vangaren zamantakewar aure, inda yanayin irin nata zaman aure kawai zai zama makaranta ga mata da yawa. A tattaunawar Blueprint Manhaja da ita, mai karatu zai ji irin gudunmawar da ta bayar ga al’umma da ma rayuwar siyasar mijinta. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Hajiya Halima Ahmad Dahir.

BLUEPRINT MANHAJA: Mu fara da jin tarihinki a taƙaice.
HAJIYA HALIMA: Sunana Hajiya Halima Ahmad Dahir, ana yi min laqabi da Kwatam Kilba, wato sarauniyar Kilba.
An haife ni a garin Jos a shekara ta 1976, kuma na yi karatuna na firamare, sakandare da kuma jami’a duk a cikin garin na Jos.
A ɓangaren aiki kuwa, na yi aikin jarida ne, inda na fara da aiki na wucen-gadi a NTA, sannan na zo na yi aiki a AIT. A taƙaice na yi aiki a rediyo da talabijin, tun daga matakin mai gabatarwa har zuwa matakin manaja. Zuwa yanzu kuma Ina aikin cin gashin kai a aikin jarida, wato ‘yar jarida mai zaman kanta, freelancer a turance. Baya ga haka, Ina tava wasu sana’o’in daban-daban, kamar siyar da gidaje, filaye da sauransu.

A ɓangaren aikin jarida, sau da yawa mata musamman ‘yan Arewa da ke aikin jarida ke ƙorafin yawaitar ƙalubale a tafiyar aikin nasu. Shin ko a na ki ɓangaren kin ci karo da hakan?
Gaskiya wannan zancen haka ne, duba da yanayin aikin. A wasu sana’o’in ma mace na fuskantar ƙulubale ballantana aiki irin na jarida. Na fuskanci matsaloli da dama a aikin, sai dai cikin ikon Allah, kinsan shi abu duk yadda ka ɗauki kanka, haka zai zo ma. A cikin kowacce sana’a ma haka ne. Kinga ni lokacin da na fara aikin na tsinci kaina ne a tsakiyar maza, kusan ni kaɗai ce mace a ɓangaren na mu.

To kinga ko ta nan dole a samu ‘yan ababen da ba a so ba. Abu na biyu, da tafiya ta yi tafiya, sai ya kasance na samu ɗaukaka, duk da cewa akwai waɗanda na tarar a wurin, amma sai aka wayi gari ni ce shugabar su. Wato kin san matsalar da mata ke samu, musamman ma a Arewa, bisa ga al’adu da kuma addini, mace dole ta ɗan samu damuwa kan kasancewar ta mace mai aiki.

Duk da cewa sau da yawa matsalar tauye mata ba faɗar addini ba ne, akwai da dama da al’adu ne da kuma ra’ayi. Magana ta gaskiya, mafiya yawan waɗanda ke kushe da hana mata neman na kai, mutane ne da ba su yi zurfi a ilimin addini ba, ko kuma tsabagen son kai ya masu yawa.

Abu na biyu kan dai zancen da na ke yi shine, a irin wannan lokaci da mu ka samu kan mu a ƙasar nan ana da rauni wurin ba wa mace girma da darajar da ta cancanta, kuma ba a cika son ba wa mata dama su nema, har su kai ga cin gashin kansu ba, kuma su taimaka wurin samun cigaba a al’umma. Wannan ne dalilin da ya sa ake kai jajirtattun mata ƙasa, saboda irin tasgaro da suke samu a tafiyar burinsu.

Maza da dama ba su yarda ya dace gare su su zauna ƙarƙashin mace ta ɓangaren aiki, a wurinsu bai kamace su ba. Ko su yi gogayya da ke ba, ko su ba su umurni su bi ba. Wannan na daga cikin matsalolin da na fuskata a lokacin da na zama sama da wasu kamar yadda na faɗa a baya.

Na samu matsaloli da yawa, sai dai inda na samu sauƙi fiye da na sauran mata shine, Allah Ya ba ni iyayen gida na alfahari, kuma duk inda na je Ina samun iyayen gida. Kuma iyayen gidan na wa na saka ni a hanyoyin da suka dace.

Kamar yadda kika ce, kin taka tsanin da har ya kai ki ga babban matsayi a aikin na jarida. Mata a wannan ɓangaren da dama na koken ana tauye su ko sukan fuskanci matsaloli da ke hana isa babban matsayi a aikin. Shin kina ganin hakan na da alaƙa da zamewarsu mata ne, ko kuwa rashin jajircewar su ne?
Eh to, a nan idan zan ce mata ba sa samun damar kai wa sama a aikin jarida, to zan iya cewa watakila rashin jajircewar su ne. Domin idan za mu wa aikin jarida adalci, idan mace ta dage a aikin, ta samu ƙwarewa, ba abin da zai hanata kai wa sama. Bari in ba ki misali da kaina, na shiga aikin jarida a matsayin mai gabatarwa, amma kinga na zo na zama mai yaɗa labarai, na zama furodusa, na zama edita, na kuma zama maketa (marketer). Dukka na yi. Kinga a nan me ya kai ni shiga dukka ɓangarorin, in ce jajircewa.

Na kai lokacin da ni na ke samar da labarai na Hausa da Turanci. Saboda lura da ana ɓata min lokacin, saboda sai na jira an yi na Turanci kafin ni in ɗauka in fassara, sai aka kai da lokacin da ni ke samar da labaran na Turanci kafin kuma in zo in fassara. Wani sa’in ma idan ta kama har na Turancin ni na ke karantawa. A nan kina ganin ta ya za a iya tauye ni.

Baya ga haka, na kasance Ina jajircewa wurin ƙirƙiro shirye-shirye masu kyau da ma’ana, kuma in yi iya kutsen da zan iya wurin ganin na tallata su, na samo masu ɗaukar nauyin su. Kuma Ina ƙirƙiro shirye-shirye da za su karɓu ga mutane, har aka kai lokacin da ba wani da ke kawo wa gidan rediyon da talabijin ɗin kuɗin shiga kamar yadda na ke.

To a nan ta ya za a iya tauye ni. Baya ga haka, na kame kaina, wanda shi ne babban abinda zai kai ki ga nasara, ban zubar da mutuncina na ‘ya mace ba. A taƙaice dai idan kika buɗe ido a aikin, kika kutsa ta kowanne ɓangare, kika koya, kika iya, kika zama gwana, ba abin da zai hana ki kai wa sama. Ko da an so tauye ki ma, ba zai yiwu ba.

Mu koma ɓangaren iyali. Akwai?
Ina da mijina, Alhaji Ibrahim Garba Dauda, wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka fito neman tsayawa takarar shugaban qasa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC, sai dai Allah bai sa ya yi nasara ba. Kuma Ina da ‘ya’yana guda shida, ciki kuwa har da ‘yan uku da na haifa, mata biyu da na miji ɗaya.

Wasu na ganin taura biyu bata taunuwa a lokaci ɗaya. Shin ta yaya kike iya haɗa harkokin neman na kai, aikin jarida da kuma kula da iyali?
To, kusan zancen haka yake, kula da iyali ba ƙaramin aiki ba ne. Sai dai iya haɗa kula da iyali da neman na kai ya tattara ne ga ra’ayin macen. Idan kika so za ki iya, musamman ma a wannan zamani da komai ya koma kan waya. Ina a gida zan iya yin kusan duk sana’o’in da na ke yi. Za a turo min, ni ma in tura wa masu siya, mu yi ciniki duk a waya, kafin in tura ɗaya daga cikin yaran da na ke da su da ke yi min aiki, a je a gani.

Idan an zo biya ma dai ta asusun bankina kuɗin za su shiga. A taƙaice dai zan iya wata ban fita ba, kuma Ina sana’a.

To ta ɓangaren aiki kuma kinga wannan daban ne, to shima dai ya danganta da tsarin da za ki yi. Za ki tsara rayuwar aikin da kuma gida ta yadda komai zai tafi yadda ake so. Kowanne ki ba shi lokacinshi.

Mu taɓo ɓangaren matsayin siyasar miji ga matarsa. Wasu matan na ganin babu ta hanyar da za su iya ba wa mazajensu gudunmawa a lokacin da suka fito takara, shi ya sa wasu lokuta sukan zama ‘yan kallo. Shin ta wacce hanya ce kike ganin mata za su iya taimakawa mazajensu a siyasa?
Eh to, a wannan ɓangaren dai ba za a ce maza ba su da laifi ba, kuma su ma matan ba a rasa na su. Wani namijin bai ɗauki mace a matsayin komai ba face matar gida mai kula da shi da ‘ya’yansu. Ba ya maganar komai da ya shafi al’amurranshi na yau da kullum. Laifin kenan na vangaren maza.

A ɓangaren mata kuwa, za ki samu wasu mata suke hana mazajensu aikata hakan ko da kuwa suna son yi. Saboda rashin nuna damuwa da sha’anin da ya shafi mazajensu.

Bari in ba ki misali da kaina, tsakani da Allah, Allah Ya ba ni miji da duk abinda ya shafe shi na wa ne. Saboda ba ni da wani mahaluƙi da na ke da kusanci da shi kamar sa.

Mu na da shaƙuwa da fahimtar da komai na sa na sani, ko da kuwa zai yi ba daidai ba, a misali zan ma ki, to zai iya gaya min. Ba ma ɓoye wa juna duk abinda ya shafe al’amurranmu. Komai na sana’ar sa na sani.

Kuma zan iya tsaya masa a lokacin da ba ya nan. Inda ake buƙatar sa hannunsa ma zan iya sa wa a madadinsa. Sai dai fa ba komai ne zai iya kawo hakan ba sai yadda dukkanmu mu ka ɗauki junanmu.

Sai siyasarsa kuwa, taka rawa da na yi na da alaƙa da yanayin aikina. A matsayina ta ‘yar jarida, aikina yana da amfani ga tafiyar siyasarsa. Domin kusan kashi 80 na aikin na ‘yan jarida ne. Kamar yadda wani ogana yake ce masa, “kai ka samu bulus. Aikin da za ka biya maƙudan kuɗaɗe a yi ma, ga shi a gidanka.”

Kuma dama ni a aikin jarida na fi ƙwarewa a tallata ‘yan siyasa, don na yi aiki da ‘yan siyasa da dama.

Hajiya Halima

Rawar da mace za ta iya taka wa a harkokin mijinta ba wai sai siyasa ba, ya ta’allaƙa ne da yadda ita matar ta gabatar da kanta. Wani lokacin ba laifin mazan ba ne, wasu mata a gidan mijin ba abinda suke tunani sai nawa mazajensu suka tara, mai za su iya yagga daga wurinsa, kuma nawa za su iya mallaka a matsayin gado. Ba sa tunanin yadda za su ba da ta su gudunmawar a bunƙasar arzikin.

Yanzu akwai matan da ko magi ne babu a gida sai sun jira miji ya dawo ko da kuwa suna da kuɗin da za su iya siya. A gaskiya ni yadda na fahimci ma’anar aure ya bambanta da yadda mata da yawa suke kallonshi, dalilin kenan da ya sa suke min kallon wawuya wanda a wurina wannan ne na wa wayon.

Saboda ni ban ɗauki miji a matsayin miji kawai ba, Ina ɗaukar mijina a matsayin ɗan’uwana, ubana, abokina. Sau da yawa na ke ajiye mijin a gefe, mu koma ta ƙawaye, a yi fira ana kashe hannu, a taƙaice dai mijina shi ne babban abokina.

Sai kuma an zo maganar auren sai in ɗauko rigar miji in ɗora masa wurin ladabi da biyayya. Amma akasarin mata suna tsayawa ne a iya ɓangaren zamantakewar aure. Ba sa kai tunaninsu ga yadda za su iya taimakawa sana’ar mijinsu.

Daga ƙarshe wane kira za ki yi ga mata masu zaman kashe wando?
Maganar gaskiya zamani ya wuce da mata za su zauna su ce duk wata ɗawainiya ta su tana kan mijinsu. Duba da yanayin canzawar rayuwa, gaskiya ana buƙatar taimakekeniya a tsakanin ma’aurata, duk da cewa wani sa’in ba laifin matan ba ne, mazan ne ba sa ba su dama saboda wasu dalilai.

Amma dai matan ya kamata su miqe, su nemi hanyar neman na kai wadda za ta yi daidai da ra’ayin mijinki, musamman a wannan zamanin na waya. Ku sani mai sana’a ta fi daraja ko a idon miji.

Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.