
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Gine-gine da Ci-gaban Birane, Ahmed Ɗangiwa, ya jaddada cewa ayyukan Ajendar Sabonta ƙasa na Shugaban ƙasa za a yi su ne bisa tsare-tsaren kwangiloli, ya na mai cewa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen soke duk wata kwangilar aiki mara ƙarko da suka gano ba.
Ɗangiwa ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar gani da ido wajen aikin wasu gidaje 1,500 da wasu 500 a Kano waɗanda ake yin su a ƙarƙashin haɗakar jama’a da kuma abinda Kasafi ya ware, ya na mai kira ga masu aikin da su tabbatar da yin ingantattu.
Ya ce, ba za su lamunci duk wani aiki mara ƙarko da aka yi ba, waɗanda ke ƙarƙashin ajandar Shugaba Bola Tinubu na sabonta ƙasa a ko’ina a Nijeriya.
Ya kuma ce, matuƙar suka samu wani ɗan kwangilar da ya yi aiki mara nagarta, to za su rushe shi tare da umartar sa da ya sake wani mai kyau ko kuma a soke kwangilar daga hannunsa.
Ministan ya ƙara da cewa, gine-ginen gidaje na tasiri ga tattalin arziƙi wajen bada damar samun kuɗi ga leburori da masu sana’ar sayar da abinci da kayayyakin gini da makamantansu.
Kazalika, Ministan ya umarci masu kula a mataki na tarayya da wakilta jami’in ma’aikatarsu da su kula da gudanar da ayyukan don tabbatar da samun masu inganci da kuma kammala su akan lokaci.