Daga AISHA ASAS
Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello, ya ƙaddamar da shirin yaƙi da karya dokokin hanya a birnin Abuja a matsayin wani mataki na tabbatar da jama’a na kiyaye dokokin hanya yadda ya kamata a cikin birnin.
Ƙaddamar da shirin ya auku ne a ƙarshen makon da ya gabata a Abuja.
A lokacin da yake jawabi a wajen taron ƙaddamarwar, Bello ya tunatar da mazauna Abuja cewa dukkanin ƙa’idoji da alamomin da aka sanya a hanyoyi, an yi hakan ne da nufin kare rayukan masu amfani da hanyoyin da kuma hana cunkoso.
Yana mai cewa, duba da yadda ake ta samun bunƙasar jama’a a birnin Abuja, an fahimci mutane da dama ba su san kan dokokin amfani da hanyoyi ba.
Daga nan ministan ya yi jinjina ga Hukumar Kiyaye Haɗurra da sauransu, bisa irin ƙoƙarin da suke yi wajen kula da hanyoyin Abuja.
Sanarwar manema labarai da sakataren labarai na hukumar Abuja, Mr Anthony Ogunleye ya fitar, ta nuna dukkanin hukumomin da lamarin ya shafa sun bada tabbacin za su bada cikakken haɗin kansu don shirin ya cim ma nasara.
Taron ya samu halarcin jami’ai da hukumommi daga ɓangarori daban-daban.