Minista Dare ya ƙaddamar da gasar ‘Principal Cup’

Daga BASHIR ISAH

An ƙaddamar da gasar ƙwallon ƙafa na ‘Principal Cup’. Ministan Matasa da Wasannin Motsa Jiki, Mr Sunday Dare ne ya ƙaddamar da gasar a birnin Legas a wannan Juma’a.

Bayan ƙaddamar da gasar, Igbobi da kuma Government College Kaduna, su ne suka fara fafatawa a filin wasannin motsa mitsa jiki na Agege, Legas.

A cewar Minista Dare wanda shi ne silar farfaɗo da gasar ‘Principal Cup’, ” Cikar buri ne kuma abin farin ciki ganin wannan gasa ta kankama a yau.

“Muna alfahari da wasan da waɗannan matasa suka yi a yau. Ina fata wannan zai zama wata hanya ta gano matasa masu fasahar wasan ƙwallo waɗanda nan gaba za su zama tamkar irin su Daniel Amokachi , Franklin Howard, Tajudeen Disu, Waidi Akanni waɗanda a gabansu aka ƙaddamar da gasar don ƙarfafa wa ‘yan bayansu gwiwa.”

Ya ci gaba da cewa, “Gasar ta assasa abota da kuma wanzar da haɗin kai a tsakanin masu gasa, don haka muke so mu dawo da martabar gasar, ta wannan hanya ne fitattun ‘yan ƙwallo Segun Odegbami, Daniel Amokachi, Henry Nwosu, Tajudeen Disu , Ali jeje suka soma har ya kai ga duniyar ƙwallo ta san da su.”

Ministan ya ce yanzu dai ya tabbata an farfaɗo da gasar ‘Principal Cup’, don haka akwai buƙatar ɗalibai su haɗa sha’anin ƙwallo da karatu.

Taron ƙaddamarwar ya samu halarci baƙi na kusa da nesa, ciki har da Mataimakin Gwamnan Edo, Comrade Phillip Shaibu, Ƙaramin Ministan Ilimi Chief Emeka Nwajiuba, Mataimakin Hukumar NFF Barr. Seyi Akinwunmi, Shehu Dikko, Daniel Amokachi da dai sauransu.