Minista Lai ya saci jiki zuwa Amurka don ganawa da shugabannin Tiwita

Sahihan rahotanni sun tabbatar da Ministan Yaɗa Labarai da Raya Al’adu na Nijeriya, Lai Mohammed ya tafi Ƙasar Amurka musamman don ganawa da shugabannin kamfanin Tiwita.

Cikin wani hoton bidiyo da aka yaɗa jiya Talata, an ga Minista Lai tare da Olusegun Adeyemi wanda hadimi ne na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga ga Shugaban Ƙasa, a cikin jirgin sama na Delta Airline za su keta hazo zuwa Amurka.

Idan dai za a iya tunawa a ranar 5 ga Yulin da ya gabata ne Gwamnatin Nijeriya ta haramta wa kamfanin Tiwita gudanar da harkokinsa a Nijeriya baya da Tiwita ta goge wani saƙon da Shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa ns Tiwita.

Saƙon da Buhari ya wallafa a wancan lokaci inda ya gargaɗi jama’ar yankin Kudu kan ƙudurinsu na neman a raba ƙasa ya haifar da zazzafar muhawara a ƙasa, inda ya yi barazanar ɗaukar mataki a kan jama’ar yankin ta hanyar amfani da yaren da suka fi fahimta.

Sai dai gwamnati ta yi iƙirarin cewa matakin dakatar da Tiwita da ta ɗauka na da nasaba da yadda ake amfani da dandalin wajen yaɗa labaran ƙarya da yi wa haɗin kan ƙasa barazana da sauransu wanda hakan ka iya tada zaune tsaye.

Bayanai sun ce an ga Lai Mohammed a cikin bidiyon sanye da hula hana-salla domin ɓadda kama inda ya zauna a kujera mai lamba 8A a cikin jirgin Delta Airline wanta ya bar Legas zuwa New York.