Minista Sadiya ta ƙaddamar da shirin N-Power kashi na uku

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin nan na bai wa matasa tallafin fara sana’a mai suna N-Power.

Mutum 510 aka ɗauka a wannan matakin shirin a jihohi 36 da Gundumar Birnin Tarayya (FCT).

Lokacin da ta ke ƙaddamar da zangon ‘C’ na shirin, wato ‘Batch C’ a ranar Litinin a ɗakin taro na NAF Conference Centre da ke Abuja, Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta taya masu cin moriyar shirin da su ka yi nasarar shiga wannan matakin waɗanda aka ɗauka murna, sannan ta shawarce su da su yi amfani da wannan damar da aka ba su.

Sadiya Umar Farouq ta yi la’akari da cewa an yi wasu sauye-sauye a tsarin zaɓen masu cin moriyar N-Power kuma ta sha alwashin cewa ma’aikatar ta ta ƙudiri aniyar tabbatar da cewa za a cimma dukkan manyan muradan da aka tsara na shirye-shiryen inganta rayuwa na tarayya (National Social Investment Programmes).

Ta ce, “An shigo da wasu sababbin dabaru cikin zaɓen ‘yan shirin N-Power da hanyar biyan su kuɗi wanda ya haɗa da ƙirƙiro tsarin gudanar da harkar inganta rayuwa na ƙasa, wato ‘National Social Investment Management Systems’ (NASIMS), haɗin gwiwa da manyan hukumomin gwamnati irin su NYSC, UBEC, NPHCDA, NOA da wasu masu yawa, waɗanda tare da su ne ma’aikatar mu ke tafiya sosai don aiwatar da shirye-shiryen ta.

“Don tabbatar da magance matsalar sadarwa, dangane da takurar tafiyar saƙwanni, faɗaɗar intanet a ƙasar nan, wannan ma’aikatar ta samar da hanyar samun bayanai ta manhajar USSD. Taƙaitacciyar kalmar USSD ɗin, wato *45665# ita ce za ta bayar da haɗin intanet da mutum ke buƙata da kuma tallafin jami’an kimiyya don samun isa ga ayyukan bada bayanai ga masu cin moriyar shirin mu.”

Ministar ta gode wa Shugaba Muhammadu Buhari saboda hoɓɓasan da gwamnatin sa ke yi wajen kawar da fatara a ƙasar nan tare da ci gaba da Shirye-shiryen Inganta Rayuwa na Ƙasa (NSIPs).

Ta kuma gode wa membobin Majalisar Tarayya saboda yadda su ka amince a kashe kuɗaɗe kan shirin na N-Power tare da aikin sa ido da su ke yi don tabbatar da cewa ana aiwatar da shirin kamar yadda aka tsara.

Minista Sadiya ta raba takardun kama aiki ga wasu daga cikin waɗanda su ka samu nasarar shiga shirin.

Ƙaramar Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Ambasada Mariam Yalwaji Katagum, da Ministar Harkokin Mata, Uwargida Pauline Tallen, da Rasdan kuma babban Kodinetan Harkokin Agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Edward Kallon, tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Amayanabo na Twon-Brass a Jihar Bayelsa, Alfred Diette Spiff, da sauran manyan mutane su na daga cikin waɗanda su ka yi jawaban sa alheri a wajen taron.

Fitaccen mawaƙin nan mai suna D’banj kuma ya nishaɗantar da mahalarta taron.

Shi dai zangon ‘Batch C’ na shirin N-Power, an raba shi ne zuwa matakai biyu. Matakin C1 ya ƙunshi masu cin moriyar shirin mutum 510,000 yayin da matakinwhile stream C2 ya ƙunshi mutum 490,000.

A ƙarƙashin Batch C1, an zaɓi jimillar mutum 450,000 don su amfana a ƙarƙashin sashen waɗanda su ka kammala karatun jami’a, sai mutum 60,000 marasa digiri.

Shirin N-Power, wanda ya ɗora fifiko kan Aikin Gona, Kiwon Lafiya harkar Konfuta da Intanet (ICT), Kasuwanci da Gine-Gine, ana shigar sa ne ta hanyar cike fom a intanet da kuma tsarin zaɓar masu cin moriya don a tabbatar da adalci ga kowa, tare da tsare gaskiya da inganci wajen ɗaukar masu cin gajiyar sa.