Minista Sadiya ta yi jimamin kisan gilla a Borno

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana alhini kan kisan gillar da ‘yan ta’adda su ka yi wa manoma 43 a Jihar Borno, ta na mai bayyana kisan da cewa mummunan aiki ne da kuma rashin tausayi.

Aƙala manoma 43 aka yi wa mummunan kisa a ƙauyen Zabarmari da ke cikin Ƙaramar Hukumar Jere ta Jihar Borno a ranar Asabar a fadamun shinkafa, yayin da aka bada rahoton cewar mutum shida sun ji rauni. An bayyana cewa kusan dukkan su ‘yan Jihar Sokoto ne da su ka je cirani a fadamun shinkafa.

Hajiya Sadiya ta yi magana ne a cikin wata takardar saƙon ta’aziyya da ta aika wa da gwamnatin Jihar Borno.

A takardar, ministar ta yi wa al’ummar jihohin Borno da Sokoto da gwamnatocin jihohin ta’aziyyar abin da ya faru.

Ta ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya za ta yi dukkan abin da za ta iya wajen kawo ƙarshen hare-haren da masu tsattsauran ra’ayi ke kaiwa, kuma ta roƙi Allah da ya kare jama’a.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*