Ministan Ƙwadago ya bada tabbacin samun daidaito tsakanin gwamnati da ƙungiyar ASUU

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan yi a Nijeriya, Mista Chris Ngige ya na sa ran ƙungiyar ASUU ba za ta shafe tsawon wata guda tana yajin aiki ba.

Dr. Chris Ngige yi wannan bayanin ne ga manema labarai bayan ya tashi daga wani taro da ya yi da shugabannin ASUU a Abuja.

Dr. Chris Ngige ya ce sun cin ma matsaya a kan wasu abubuwa da dama, kuma an tsaida lokacin da za a aiwatar da alƙawuran da gwamnati ta yi wa ƙungiyar.

A cewar ministan, wakilan ASUU sun yarda su tuntuɓi ‘ya‘yansu domin jin ta bakinsu, idan sun amince da tayin da aka yi masu, za su koma kan aiki.
Kamar yadda The Guardian ta rahoto a ranar Laraba, Ministan ya ce an yi magana kan yarjejeniyar (MoA) da aka sa wa hannu kafin a koma aiki a 2020.

“Abubuwa ɗaya zuwa biyu suka rage mana. Daga cikin sababbin abubuwan shi ne jin batun halin da ma’aikata suke ciki.”

An yi yarjejeniya a 2009 duk bayan shekaru biyar za a duba halin da ma’aikata suke ciki. Tun 2014 aka yi na ƙarshe,” inji Ngige.

Ngige ya yi bayanin abin da ya kawo cikas wajen cika wannan alƙawari, amma ya bayyana cewa an kafa wani sabon kwamiti da zai yi aiki a kan maganar albashi.

Amma ministan ya gargaɗi malaman jami’ar cewa ba za su kawo abin da ya saɓa wa tsarin NSIWC ba, wanda ita ce hukumar da ke tsaida albashin ma’aikata.

Ƙungiyar ASUU ta reshen Jami’ar Bayero da ke Kano ta ce ka da a janye yajin aikin sai an cika duka alƙawuran da aka yi a 2020.

Akwai alamun cewa yajin aikin zai iya wuce yadda ministan yake tunani. Wani malami a ABU Zariya ya ce idan ba su gani a ƙasa ba, ba za a buɗe ɗakunan karatu ba.

Idan ba a manta ba, Ministan Ƙwadago da samar da Ayyukan yi, Chris Ngige ya yi wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ƙarin haske kan tattaunawar da a ke yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da ƙungiyar malaman jami’o’i.

A tuna cewa ASUU ta shiga yajin aikin gargaɗi na tsawon wata guda tun ranar 14 ga watan Fabrairu saboda gazawar gwamnati wajen cimma yarjejeniyoyin da aka yi da ita.
Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan kammala taron, ministan ya ce shugaban ƙasar ya gamsu da bayanin da ya yi masa.

Ya ce, “za mu aiwatar da yarjejeniyar 2020 da a ka yi da ASUU,” a cewar sa, gwamnatin tarayya ta biya Naira biliyan 40 na alawus-alawus da kuma Naira biliyan 30 domin walwalar malaman.

Ya ƙara da cewa an kuma biya Naira biliyan 22.7 da ga ƙarin kasafin kuɗi sannan a ka ba su alawus-alawus na 2021.