Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya yi kira ga rundunar sojan sama ta Najeriya da ta ƙara ƙoƙari wajen mamaye sararin samaniya da kawo ƙarshen rashin tsaro a Nijeriya, musamman a yankin Arewa maso Yamma, yana cewa, “Don Allah, ku kawo ƙarshen rashin tsaro yanzu.”
Da yake ziyarar hedkwatar rundunar sojan sama ta 213 Forward Operating Base a Jihar Katsina, Ministan ya bayyana cewa, “Muna tura ƙarin kayan aiki, ciki har da jiragen helikwafta na yaki da na’urorin jirgi marasa matuƙa domin ƙara inganta iya aikinku da kawar da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda. Shugaban ƙasa yana farin ciki da nasarorin da kuke samu kuma zai samar da kayan aiki da kuma tallafin jin daɗin ku.
Game da wa’adin kawo ƙarshen rashin tsaro, Ministan ya ce, “Ku kawo ƙarshen shi yanzu, don Allah. Ku kawo ƙarshen rashin tsaro yanzu.”
Tun da farko, yayin da yake jawabi ga manyan jami’ai da dakarun FOB Zurmi da Gurbi Baure, ya yaba musu bisa sabbin himmarsu wajen yaƙi da rashin tsaro a yankin.
Ya ce, “Na gan ku kuna da ƙwarin guiwa. Kuma nasarorin da muke samu a yanzu suna nuna cewa kuna da ƙwarewa da ƙarfin hali don kawo ƙarshen wannan lamarin. Mun zo ne don mu gode muku bisa ƙoƙarin da kuka yi kawo yanzu. Tare da jajircewarku a cikin ‘yan watannin nan, ana samun ci gaba a kullum, kuma na yi imanin cewa za a kawo karshen rashin tsaro cikin hanzari.”
Sanarwa daga Ma’aikatar Tsaro ta ambaci Ministan yana yaba wa jihohin Zamfara da Katsina bisa goyon bayan da suke ba wa gwamnatin tarayya wajen yaƙi da rashin tsaro a yankin.
Ya ce, “To, na yi imanin duk jihohin suna bada goyon baya. A farkon makon nan, mun yi taro tare da gwamnonin Katsina da Zamfara da kuma mai ba wa shugaban Ƙasa shawara kan tsaro domin tsara yadda za a kawo ƙarshen rashin tsaro a waɗannan jihohi da Arewa maso Yamma baki ɗaya. Kuma na yi imani cewa, tare da sabon umarni, muna da tabbacin cewa za a kawo ƙarshen rashin tsaro nan ba da jimawa ba.