Ministan yaɗa labarai zai shugabanci taron IPI

An sanar da cewa Ministan yaɗa labarai na Nijeriya, Mohammed Idris, zai jagoranci taron shekarar 2024 na reshen Nijeriya na International Press Institute (IPI) wanda za a gudanar a ranar Laraba a birnin Abuja. Wannan sanarwa ta fito daga bakin Ahmed I. Shekarau, sakataren IPI Nijeriya, a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin.

Sanarwar ta bayyana sunayen fitattun baƙi da suka tabbatar da halartar taron, ciki har da mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, tsohon gwamnan Jihar Ogun, Olusegun Osoba, mai wallafa jaridar Vanguard, Sam Amuka Pemu, Shugaban ƙungiyar masu jaridu ta Nijeriya (NPAN) Kabiru A. Yusuf, mai ba wa Shugaban Ƙasa shawara Bayo Onanuga da darakta janar na hukumar wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) Lanre Issa-Onilu.

Hakanan, za a halarci taron daga fitattun mutane kamar Daraktan Afrika na MacArthur Foundation Kole Shettima, Daraktan CARE Hussaini Abdu, mai wallafa Jaridar ThisDay/Arise Nduka Obaigbena, tsohon ministan yaɗa labarai Lai Mohammed da Farfesa Abiodun Adeniyi na Jami’ar Baze. Za a gudanar da taron ne a Otel ɗin Abuja Continental (da aka fi sani da Sheraton Hotel) tare da babban taron shekara-shekara da za a yi ranar Alhamis 12 ga Disamba.

Sanarwar ta ƙara da cewa fitaccen malamin yaɗa labarai Farfesa Tonnie Iredia zai gabatar da jawabi kan “Dimokraɗiya, ‘yancin jaridu da muhimmancin kare wuraren jama’a na Nijeriya ” a taron. Hakanan, kwamitin ƙwararrun ‘yan jaridu za su tattauna kan wannan jawabin tare da jagorancin Busola Ajibola, ƙwararriyar mai kare ‘yancin jarida.

Daga cikin masu magana akwai Waziri Adio, Garba Shehu da Farfesa Abigail Ogwezzy-Ndisika.

Za a yi jawabi daga Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede kan “haɗin kan jaridu da hukumomin yaƙi da cin hanci wajen yaƙar cin hanci.” Tsohon ministan yaɗa labarai Lai Mohammed zai kuma yi jawabi kan “Gwamnati da jaridu: Yadda za a rage tashin hankali, fahimtar juna da kauce wa Ƙaƙaba takunkumi.” Taron zai zama dandalin tattaunawa kan manyan matsalolin da ke addabar aikin jarida a Nijeriya tare da bayar da damar nemo mafita mai ɗorewa ga matsalolin dake fuskantar ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai.